Kano: Abdullahi T. Gwarzo Ya Bayyana Dalilin Tinubu na Tsige Shi daga Muƙamin Minista
- Abdullahi T. Gwarzo ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya sauke shi daga muƙamin minista ne saboda ya naɗa ɗan Kano ta Tsakiya
- Tsohon ƙaramin ministan gidaje da raya birane ya ce Nasiru Gawuna ya kamata a fara yi wa tayin kujerar kafin a ɗauko wani
- Abdullahi Gwarzo ya ce duk da haka ba shi da wata matsala da wanda aka ba mukamin a yanzu domin tare suke harkokin siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Tsohon ƙaramin ministan harkokin gidaje da raya birane, Abdullahi T. Gwarzo ya ce babu laifin da ya yi aka sauke shi daga muƙamin.
Ya ce dalilin sauke shi daga matsayin minista shi ne yankin da ya fito watau Kano ta Arewa na da mutane masu muƙamai da yawa a gwamnatin tarayya.
Dalilin sauke T. Gwarzo daga minista
Abdullahi Gwarzo ya ce wannan dalilin ne ya sa aka tsige shi daga muƙamin domin a bai wa ɗan yankin Kano ta Tsakiya wanda aka ce ba a basu muƙamai sosai ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon ministan ya bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa kwanaki kalilan bayan shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya maye gurbinsa da Yusuf Abdullahi Ata.
T. Gwarzo ya ƙara da cewa idan har haka ne babu wanda ya cancanta a ba muƙamin da ya wuce tsohon ɗan takarar gwamnan Kano, Nasiru Gawuna.
Gawuna ya kamata a naɗa minista
"Idan da gaske ake Kano ta Tsakiya ake so a ba, ga ɗan takararmu na gwamna nan, Dr Nasiru Gawuna, wanda shi ne jagora a Kano ta Tsakiya, me ya hana a ba shi?"
"Kuma idan ka duba takwarorinsu na wasu jihohin duk an ba su minista, misali ka ɗauki ɗan takarar gwamnan APC a jihar Filato da na Zamfara, duk an ɗauko su an ba su minista."
- Abdullahi T. Gwarzo.
Ya ƙara da cewa kamata ya yi tun farko a fara yiwa Gawuna tayi, idan ya nuna baya so ne sai a ɗauko wani daban.
Abdulahi Gwarzo ya ce duk da haka wanda aka naɗa yanzu babu wata matsala a tsakaninsu kuma tare suke harkokin siyasa.
Shekarau ya gana da Abdullahi Gwarzo
A wani rahoton, an ji cewa Malam Ibrahim Shekarau ya gana da karamin ministan gidaje da raya birane da shugaba Bola Tinubu ya kora, Abdullahi Tijjani Gwarzo.
Wata sanarwa da Abdullahi Gwarzo ya fitar ta nuna cewa tsohon gwamnan Kano ya gana da tsohon ministan domin taya shi murna.
Asali: Legit.ng