Kwankwaso Ya Yi Rashi, Dan Takarar Gwamna a NNPP Ya Koma PDP a Gombe

Kwankwaso Ya Yi Rashi, Dan Takarar Gwamna a NNPP Ya Koma PDP a Gombe

  • Tsohon dan takarar gwamna a NNPP, Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki ya sauya sheka zuwa PDP a Gombe
  • Hon. Mailantarki ya koma jam'iyyar PDP ne mai adawa a jihar a yau Asabar 9 ga watan Nuwambar 2024
  • Legit Hausa ta yi magana da hadimin Hon. Mailantarki kan sauya shekar mai gidansa zuwa jam'iyyar PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Jam'iyyar NNPP ta yi babban rashi bayan dan takarar gwamna ya yi murabus daga jam'iyyar a kwanakin baya.

Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki ya koma jam'iyyar PDP a yau Asabar 9 ga watan Nuwambar 2024.

Dan takarar gwamna a NNPP ya koma PDP a Gombe
Dan takarar gwamna a NNPP, Khamisu Mailantarki ya koma jam'iyyar PDP. Hoto: Isma'il Abubakar Maisalati, People's Democratic Party, PDP.
Asali: Facebook

Yadda Mailantarki ya sha Kaye a zaɓen 2023

Wannan na kunshe ne a cikin wani bidiyo da hadimin Mailantarki a bangaren sadarwa, Isma'il Abubakar Maisalati ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Asabar.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida: Jam'iyyar NNPP ta sake taso Kwankwaso a gaba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan Hon. Mailantarki ya gaza samun nasara a zaben 2023 da aka gudanar.

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na APC shi ya lashe zaben inda ya yi nasara kan jam'iyyun PDP da NNPP.

Dan takarar PDP, Muhammad Jibrin Barde shi ya zamo na biyu yayin da Mailantarki na jam'iyyar NNPP ya kasance na uku.

Mailantarki ya koma jam'iyyar PDP a Gombe

Mailantarki ya je ofishin PDP gundumar Herwagana inda nan ne mahaifarsa da ke Gombe domin yankan katin zama ɗan jam'iyyar.

Daga bisani Mailantarki ya wuce ofishin PDP ta jiha domin jaddawawa shugabannin jam'iyyar komawarsa a hukumance.

Mailantarki ya sami rakiyar daruruwan al'umma zuwa bikin sauya shekar domin nuna masa goyon baya.

Tattaunawar Legit Hausa da hadimin Mailantarki

Legit Hausa ta yi magana da hadimin Hon. Mailantarki kan sauya shekar mai gidansa zuwa jam'iyyar PDP.

Isma'il Abubakar Maisalati ya ce Mailantarki ya shiga PDP ne domin ba da ta shi gudunmawa ba wai domin neman matsayi ba.

Kara karanta wannan

Ana daf da zabe, yan APC sun watsawa Gwamna kasa a ido, sun goyi bayan dan adawa

Maisalati ya ce Mailantarki ya dawo PDP ne domin ganin an ceto mutanen Gombe daga mugun yanayi da APC ta saka su ciki.

Kan rikicin PDP kuma, Maisalati ya ce a kowace jam'iyya akwai wannan matsala inda ya ce Mailantarki mutum ne mai daraja da biyayya ga na gaba da shi.

Ya kara da cewa a tarihin rayuwarsa, Mailantarki bai da abokin fada kuma yana siyasa babu gaba ba fada wannan shi ne takensa.

Mailantarki ya yi murabus daga jam'iyyar NNPP

A baya, mun baku labarin cewa jagoran jam'iyyar NNPP kuma dan takarar gwamnan jihar Gombe, Hon. Khamisu Mailantarki ya yi murabus.

Mailantarki ya sanar da yin murabus din ne a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024 a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu.

Sakataren jam'iyyar NNPP a Gombe, Muhammad Baba Sherrif ya yi magana kan murabus din inda ya ce jam'iyyar ta yi rashin jigo mai hidima gare ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.