Tsohon Kwamishina Ya Koma Adawa, Ya Nemi N500m domin Daina Sukar Gwamna

Tsohon Kwamishina Ya Koma Adawa, Ya Nemi N500m domin Daina Sukar Gwamna

  • Tsohon kwamishina ya juye da adawa inda ake zargin ya fara neman kudi domin tsagaita wuta kan sukar gwamna
  • Fabian Ihekweme da ya yi kwamishina a mulkin Hope Uzodinma a wa'adin farko, ya koma adawa da ya rasa kujerarsa
  • Gwamnatin Imo na zargin Ihekweme da neman kudi daga Uzodinma da abokansa domin barin caccakarsa da yake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Imo - Gwamnatin jihar Imo ta bankado shirin wani dan adawa kan neman kudi daga Hope Uzodinma.

Gwamnatin Imo ta ce dan adawar wanda tsohon kwamishina ne da ya yi kaurin suna wurin caccakar Hope Uzodinma na neman a biya shi domin ya bari.

Kara karanta wannan

'Zan dauki mataki': Abba ya magantu kan shirin yin garambawul, kwamishinoni sun tsorata

Tsohon kwamishina ke neman kudi a hannun mukarraban gwamna
Gwamnatin Imo ta zargi tsohon kwamishina da sukar Gwamna saboda neman kudi. Hoto: Hope Uzodinma.
Asali: Facebook

Ana zargin Ihekweme da sukar gwamna saboda kuɗi

Kwamishinan yada labarai a jihar, Declan Emelumba shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da Vanguard ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Emelumba ya ce Dakta Fabian Ihekweme ya tuntubi wasu na kusa gwamnan kan a ba shi wasu kudi domin yarjejeniya kan abin da yake yi.

Duk da kwamishinan bai bayyana yawan kuɗin da Ihekweme ya bukata ba domin dakatar da caccakar Gwamna Uzodinma wasu majiyoyi sun ce kudin ya kai N500m.

"Lokacin da muka cewa kawai neman bata sunan gwamna yake yi, mutane suka ce mun yi zafi da yawa."
"Ga shi yanzu ya tabbatar neman kudi kawai yake yi wurin cigaba da bata sunan Gwamna Uzodinma."

- Declan Emelumba

Yadda tsohon kwamishina ke neman kudi a gwamnati

Emelumba ya ce Ihekweme ya tuntubi da yawa daga cikin abokan Uzodinma kan kudurinsa na neman kudi a cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

'Ban tsoron EFCC': Gwamnan PDP ya bugi kirji, ya fadi abin da zai yi idan suka neme shi

Ya ce na karshe da ya tuntuba wani dan kasuwa ne da ke Lagos inda har ya tura masa lambar asusun banki.

Kwamishinan ya ce mutumin ya bukaci biya masa tikitin jirgi zuwa Lagos domin tabbatar da yarjejeniyar tsagaita cin mutuncin Uzodinma.

Uzodinma ya fadi ni'imomin Najeriya

Kun ji cewa Gwamna Hope Uzodinma ya taya al'umar kasar Najeriya murnar cika shekaru 64 da samun yancin kai.

Gwamnan ya ce akwai ni'imomi da Ubangiji ya yi wa kasar nan masu tarin yawa, saboda haka ya dace a yi murna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.