'Zan Dauki Mataki': Abba Ya Magantu kan Shirin Yin Garambawul, Kwamishinoni Sun Tsorata

'Zan Dauki Mataki': Abba Ya Magantu kan Shirin Yin Garambawul, Kwamishinoni Sun Tsorata

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano na shirin yin garambawul a gwamnatinsa
  • Gwamnan ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba zai sallami kwamishinoni da ba su tabuka komai ba yayin da suke ofis
  • Shirin daukar wannan mataki ya biyo bayan karbar rahoto daga kwamitin kula da ayyukan kwamishinonin a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi magana kan yin garambawul a gwamnatinsa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce masu mukamai a gwamnatinsa da ba su tabuka wani abu ba za su rasa kujerunsu.

Abba Kabir zai yi garambawul a gwamnatinsa
Abba Kabir ya tabbatar da shirin yin garambawul a mukaman kwamishinoni. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Abba ya shirya wargaza gwamnatinsa a Kano

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishina ya koma adawa, ya nemi N500m domin daina sukar gwamna

Abba Kabir ya bayyana haka ne bayan karbar rahoton kwamitin kula da kokarin mukarrabansa a gwamnatin, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce nan ba da jimawa ba al'umma za su ji matakin da zai sauka game da wasu daga cikin kwamishinoni.

Har ila yau, Abba ya ce kafin nada su mukamansu ya tabbatar da bin kwarewa da gogewa kan aikinsu, Daily Post ta ruwaito.

"Abin da nake bukata daga gare ku" - Abba

Abba ya ce babu ɗaya daga cikinsu da ya bi kafa ko ya turo aka nema masa alfarma domin ba shi mukamin kwamishina.

Har ila yau, Abba ya ce abin da yake tsammani daga kwamishinonin shi ne biyayya gare shi da NNPP da kuma tafiyar Kwankwasiyya.

Sannan kuma ya ce akwai bukatar himmtuwa kan aiki da kawo tsare-tsare da za su ciyar da jihar Kano gaba ta ɓangarori da dama.

Kara karanta wannan

'Ban tsoron EFCC': Gwamnan PDP ya bugi kirji, ya fadi abin da zai yi idan suka neme shi

Gwamnatin Kano ta magantu kan cire manyan sakatarori

Kun ji cewa Gwamnatin Kano ta yi martani kan zargin alakar siyasa da sauye-sauyen ma'aikatu da aka yi wa wasu manyan daraktoci da sakatarori.

A wata sanarwa ta musamman, gwamnatin ta ce sam babu kamshin gaskiya kan abin da ake yadawa cewa rikicin NNPP ta jawo haka.

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin rigima ta barke a jam'iyyar NNPP da kuma tsakanin Abba Kabir Yusuf da Kwankwasiyya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.