Sanata Ndume Ya Samu Kariya bayan Taso Shi a Gaba kan Sukar Kudirin Tinubu

Sanata Ndume Ya Samu Kariya bayan Taso Shi a Gaba kan Sukar Kudirin Tinubu

  • Mutanen Kudancin Borno sun jaddada goyon bayansu ga Sanata Ali Muhammad Ndume kan sukar kudirin haraji na Bola Tinubu
  • Sanata Ali Ndume ya sha suka bayan ya bayyana a fili cewa ba zai goyi bayan kudirin haraji da Bola Tinubu ya aika majalisa ba
  • Wata kungiya a Arewacin Najeriya ta dura kan shi tana mai bukatar a ladabtar da shi saboda kalaman da ya yi a kan shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Fitowar Sanata Ali Ndume yana sukar kudirin haraji da Bola Tinubu ke shirin kawowa na cigaba da jawo ce-ce-ku-ce.

Biyo bayan maganar da Ali Ndume ya yi, kungiyar NRC a Arewa ta yi Allah wadai da abin da Sanatan ya fada.

Kara karanta wannan

Joe Biden ya bukaci Dangote ya dawo da litar man fetur N150?

Ndume
Mutanen Borno sun ba Ndume kariya. Hoto: Ali Ndume|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mutanen Kudancin Borno sun fito sun ba Sanata Ali Ndume kariya kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar Sanata Ndume kan kudirin harajin Tinubu

Sanata Ali Ndume ya fito ƙarara ya ce zai hada kai da yan majalisa wajen yaki da bukatar Tinubu ta sauya fasalin haraji.

Lamarin ya saka wata kungiya a Arewacin Najeriya yin barazanar siyasa ga Sanatan kamar yadda aka masa a baya.

Sanata Ali Ndume ya samu kariya daga Borno

Biyo bayan barazanar da aka yi wa Sanata Ndume, kungiyar cigaban Kudancin Borno (SBCC) ta ce tana bayan Sanatan.

Shugaban kungiyar SBCC, Bulama Ali Sawa ya ce Ndume ya yi magana ne domin kawo saukin rayuwa ga mutanensa.

"Maganar a yi kiraye ga Sanata Ali Ndume saboda ya soki kudirin haraji abin Allah wadai ne.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa za su yi taron dangi domin hana bukatar Tinubu

Abubuwan da Ali Ndume ya fada su ne ra'ayin wadanda suka zabe shi zuwa majalisa.
Ya riga ya fahimci haɗarin da ke cikin kudirin haraji, shi yasa yake yaki da shi."

- Bulama Ali Sawa, shugaban SBCC

Gwamnan Bauchi ya soki kudirin haraji

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammad ya yi tsokaci kan kudirin harajin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Bala Muhammad ya ce har yanzu gwamnonin Arewa suna kan bakarsu ta yaki da bukatar Bola Tinubu na sauya fasalin haraji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng