"Ana Tunzura Ni In Yi wa Kwankwaso Butulci" Inji Abba Gida Gida

"Ana Tunzura Ni In Yi wa Kwankwaso Butulci" Inji Abba Gida Gida

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce ya shafe shekaru a tare da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso cikin kwanciyar hankali
  • Ya ce a tsawon shekaru 40 da su ka shafe tare, babu wani sabani da ta gifta a tsakaninsa da jagoran Kwankwasiyya
  • Abba Gida Gida ya ce masu kokarin hada su ba za su yi nasara ba, domin ba zai bijirewa wanda ya taimake shi a rayuwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa bai taba samun baraka da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ba.

Ya ce tun bayan sanin Kwankwaso a tsawon shekaru 40, babu wata babbar matsala da ta gifta a tsakaninsu, kuma har yanzu ya na masa biyayya.

Kara karanta wannan

'Ban tsoron EFCC': Gwamnan PDP ya bugi kirji, ya fadi abin da zai yi idan suka neme shi

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano ya musanta baraka da Kwankwaso Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamnan ya yi magana ne a karon farko tun bayan bullar tafiyar 'Abba tsaya da kafarka' a jam'iyyar NNPP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya fadi abin da ke tsakaninsa da Kwankwaso

Legit ta wallafa cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce har yanzu ya na mubaya'a ga jagorancin shugaban Kwankwasiyya na kasa, Rabi'u Kwankwaso.

Ya bayyana cewa ko bayan bullar masu zuga shi ya rabu da Kwankwaso, ya ziyarci Madugu tare da bayyana mamakinsa kan bullar tafiyar.

"Babu baraka tsakani na da Kwankwaso:" Abba

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce shi ba mai butulci ba ne, saboda haka ba zai gujewa wanda ta silarsa Allah SWT Ya ba shi mulkin Kano ba.

Abba ya kuma jaddada cewa babu gaskiya a cikin labarin da ake yadawa kan cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya na katsalandan a gwamnati.

Kara karanta wannan

"Ban sani ba sai daga baya," Gwamna Abba ya faɗi abin da ya faru da yaran Kano

Tsaya da kafarka: Abba ya yi martani mai kaushi

A baya mun ruwaito cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi martani kan tafiyar 'Abba tsaya da kafarka' da ke neman ya bijirewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Ana zargin wasu jiga jigan NNPP,daga ciki har da Sakataren gwamnatin Kano, Baffa Bichi da jam'iyyar ta dakatar ne su ke rura wutar baraka tsakanin jagororin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.