"Tsaya da Kafarka": Gwamna Abba Ya Fusata, Ya Yi Maganar 'Cin Amanar' Kwankwaso
- Mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabir ya nuna ɓacin ransa kan masu kiraye-kirayen tsaya da ƙafarka, ya ce wannan cin fuska ne
- Abba ya bayyana cewa masu wannan surutun suna nufin bai ma san abin da yake yi ba duk da ɗumbin ayyukan da gwamnatinsa take yi
- Gwamman ya yi kira ga masoyansa a kowane ɓangare na rayuwa da kar su sake ambatar Abba tsaya da kafarka a Kano ko a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana shirin ɓallewa daga gidan jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce taken da ake yaɗawa na, 'Abba tsaya da ƙafarka" babban cin mutunci ne a gare shi.
Abba ya bayyana haka a wata hira da ƴan jarida wadda mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba magantu kan 'tsaya da ƙafarka'
Ya ce masu kiraye-kirayen Abba tsaya da ƙafarka ba komai suke masa ba illa cin mutunci da zagi domin suna nufin bai ma san abin da yake yi ba.
Kalaman gwamnan na zuwa ne yayin da ƴan Abba tsaya da ƙafarka suka fara yawa a jihar Kano.
Haka nan kuma lamarin ya zo a daidai lokacin da jam'iyyar NNPP ke fama da rikicin cikin gida musamman a tafiyar nan ta Kwankwasiyya.
Da yake mayar da martani, Gwamna Abba ya ce ya ɗauki masu kiran ya ci amanar Kwankwaso a matsayin masu kokarin cin mutuncinsa.
Kalaman Abba kan batun tsayawa da ƙafarsa
"Yanzu suna nufin duk abin da nake yi walau na samar da ababen walwalar jama'a, walau na kiwon lafiya, walau na noma, walau da ilimi da jihohi ke kwaiwayonmu, walau na tallafi duk ban iya ba kenan?
"Duk abin da muke yi ga shi nan jihohi da kasashe suna sha'awa ba za a yayata ba sai abin fitina wai tsaya da ƙafarka, wannan cin mutunci ne ake yi mani, ma'ana ba mu san me muke yi ba."
"Abin da ke kara ba ni mamaki, duk masu surutun nan suna ina a lokacin da Kwankwaso ke kan mulki? Ko shi ɗan jaridar da yake wannan ƙagen yana ina?"
"Ina amfani da wannan dama, in dai mutum masoyina ne, ko a gwamnati, ko a siyasa, ko a mu'amala daga yau kada gwamna ya ƙara jin tsaya da kafarka a Kano ko Najeriya."
- Abba Kabir Yusuf.
Shin da gaske Abba ya daina ɗaga kiran Kwankwaso?
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Kano ya ce jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya daina ɗaga kiran Kwankwaso ƙarya ne domin ba zai ci amanarsa ba.
Abba Kabir Yusuf ya kuma ɗauki zafi kan ƴan jarida inda aka ji yana cewa ba don yana ganin girmansu da kotu za ta raba su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng