Trump: Bola Tinubu Ya Taya Sabon Shugaban Ƙasar Amurka Murnar Lashe Zaɓe
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya zababben shugaban Amurka, Donald Trump murnar samun nasara a zaɓe
- A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu ya bukaci ƙara karfafa kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Amurka
- Tinubu ya ce yana da ƙwarin guiwar cewa Trump zai jagoranci dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a sassan duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump murnar lashe zaɓen da aka yi.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa yana fatan ƙara karfafa alakar Najeriya da Amurka a karƙashin mulkin Donald Trump, wanda ya dawo a karo na biyu.
Hadimin shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da Dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya taya Trump murnar lashe zaɓe duk da har yanzu ba a sanar da sakamakon zaɓen shugaban Amurka a hukumance ba.
Bola Tinubu na fatan dawo da zaman lafiya
Bola Tinubu ya ce yana kwarin guiwar cewa shugabancin Trump a Amurka zai dawo da zaman lafiya a sassan duniya.
Shugaban Najeriya ya kuma jaddada yiwuwar haɗin guiwa tsakanin ƙasahen biyu domin inganta tattalin arziki, samar da zaman lafiya da magance ƙalubalen da suka addabi jama'a.
Tinubu ya ce:
"Idan mu ka haɗa kai, za mu iya inganta hadin gwiwar tattalin arziki, samar da zaman lafiya, da magance kalubalen duniya da ke shafar mutanen ƙasashenmu."
"Jama'ar Amurka sun aminta da Trump" - Tinubu
A cewar Bola Tinubu, nasarar da Trump ya samu ya nuna irin amana da amincewar da jama’ar Amurka suka yi da shugabancinsa.
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa duba da shugabancin Trump tsakanin 2017 zuwa 2021, dawowarsa fadar White House za ta zama alheri ga alaƙar Afirka da Amurka.
Bisa la'akari da karfin iko da tasirin Amurka wajen tafiyar da al'amuran duniya, shugaba Tinubu ya yi imanin Trump zai maido zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Magoya bayan Trump sun fara murna
A wani labarin, kun ji cewa magoya baya sun fara murna yayin da aka fara fitar da sakamakon zaben shugaban kasa a Amurka.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump ne a gaba yayin da Kamala Harris ke binsa a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari.
Asali: Legit.ng