NNPP a Kano: Kusoshin Jam'iyya Sun Fara Nuna Shakku kan Shugabancin Kwankwaso

NNPP a Kano: Kusoshin Jam'iyya Sun Fara Nuna Shakku kan Shugabancin Kwankwaso

  • Ana ci gaba da samun sabani a tsakanin magoya bayan jam'iyyar NNPP wadanda ke cikin tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano
  • Rahoto ya nuna cewa rikicin jam'iyyar ya kara ta'azzara inda wasu ke nuna shakku kan jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso
  • Wasu jiga jigan jam'iyyar NNPP na ganin sai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsaya da kafafunsa ne zai ji dadin shugabancin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Wutar rikicin cikin gida da ta mamaye jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano na kara ruruwa ba tare da wata alama ta lafawa ba.

An ce dadaddun masu biyayya ga tafiyar Kwankwasiyya sun fara dawowa daga rakiyar Sanata Rabiu Kwankwaso kan shugabancin NNPP.

Kara karanta wannan

"Kwankwaso ba zai yafewa Abba laifuka 3 ba:" Madakin Gini ya fara tone tone

Kusoshin jam'iyyar NNPP sun fara nuna shakkun kan shugabancin Kwankwaso
Rikicin siyasa ya ta'azzara a Kano, kusoshin NNPP na shakku kan shugabancin Kwankwaso. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

'Yan NNPP na neman 'yancin Abba a Kano

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa tawayen kusoshin jam'iyyar NNPP dai shi ne babban kalubalen da har yanzu Kwankwaso ke fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce jiga jigan Kwankwasiyya a Kano, sun bukaci jagoran da ya sakarwa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf mara a shugabancin jam'iyyar.

Magoya bayan Gwamna Abba Yusuf na ganin cewa idan har gwamnatin jihar na son ta yi aiki yadda ya kamata, dole ne sai ya tsaya da kafafunsa.

Kusoshin NNPP na shakku game da Kwankwaso

Masana dai na ganin cewa tawaye da kuma shakkun da jiga jigan jam'iyyar NNPP ke nunawa kan jagorancin Kwankwaso ya samo asali daga babakeren da ya yi.

Rikicin ya kara ta'azzara jim kadan bayan dakatar da Abdullahi Baffa Bichi, sakataren gwamnatin jihar da Mohammad Diggol, kwamishinan zirga-zirga daga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta yi martani ga yan majalisun da su ka bar tafiyar Kwankwaso

An rahoto cewa an dakatar da wadannan jiga jigan saboda zargin suna rajin nemawa Gwamna Abba 'yanci daga dabaibayin da Kwankwaso ya daure shi da shi.

A hannu daya kuma, wasu jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya na zargin cewa jam’iyyar APC ce ke rura wutar rikicin da ke faruwa a jam’iyyar NNPP.

Abba ya daina daga wayar Kwankwaso

A wani labarin, mun rahoto cewa jita jita ta karade intanet cewa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya daina daukar wayar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Karin bayanai na nuni da cewa Gwamna Abba ya kaucewa haduwa da Rabi'u Kwankwaso domin su zauna kan rikicin siyasar da ya dabaibaye jam'iyyar NNPP a Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.