"Kwankwaso ba Zai Yafewa Abba Laifuka 3 ba:" Madakin Gini Ya Fara Tone Tone
- Tsohon jigo a tafiyar Kwankwasiyya, Aliyu Sani Madakin Gini ya fadi yadda Rabiu Musa Kwankwaso ke kallon gwamnan Kano
- Madakin Gini wanda ya bayyana ficewa daga tafiyar Kwankwaso ya zargi Madugu da kokarin dakile duk wani da zai yi kafada da kafada da shi
- Ya ce yanzu haka Kwankwaso ya na zargin Abba Kabir Yusuf da cin amanar da ta zarce wanda tsohon gwamna Abdullahi Ganduje 'ya yi'
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Dan majalisar tarayya mai wakilar Dala, Aliyu Sani Madakin Gini ya yi tonon silili kan barakar da ake zargin ta bulla tsakanin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da gwamna Abba Kabir Yusuf.
Aliyu Sani Madakin Gini da dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano/Kibiya/Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum sun bayyana ficewarsu daga Kwankwasiyya.
Wani bidiyo da Hon. Gashash ya wallafa a shafinsa na X ya nuna Aliyu Sani Madakin Gini ya na fadin wasu abubuwa a siyasar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai wasu abubuwa uku da ake zargin Kwankwaso ya ce Abba ya yi masa, kuma rashin ladabi ne a wurin uban gidan nasa a siyasa.
"Kwankwaso ba zai yafewa Abba ba:" Madakin Gini
Aliyu Sani Madakin Gini ya zargi jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da rashin son ya samu tsara a jagorancin siyasar Kano, kamar yadda Comrade Abiyos Roni ya wallafa a shafin X.
Madakin Gini ya bayyana cewa da kunnensa ya ji Sanata Kwankwaso ya na fadin Abba Kabir Yusuf ya tafka kura-kurai da su ka wuce wanda Ganduje ya yi, kuma ba zai yafe masa ba.
Madaki ya lissafa laifin Abba wurin Kwankwaso
Aliyu Sani Madakin Gini da ke wakiltar Dala a majalisar tarayya ya ce Kwankwaso na ganin bayyana rashin masaniya kan badakalar magunguna da Abba ya yi babban cin amana ce.
A cewar Madakin Gini, sauran laifuffukan sun hada da binciken batun kai yaran Kano karatu a kasashen waje, inda ake zargin an kai yara 400 a maimakon 1000.
Laifi na karshe kuma a cewar Aliyu Sani Madakin Gini shi ne bijirewa umarnin Kwankwaso da Abba ya yi na cewa ya kori sakataren gwamnatin Kano, Baffa Bichi.
An samu bayanin barakar Abba da Kwankwaso
A baya mun ruwaito cewa hadimin gwamnan Kano a kan kafafen sada zumunta, Salisu Yahaya Hotoro ya musanta cewa akwai wata baraka.
A wani jawabi da ya fitar a farkon makon nan, Malam Salisu Yahaya Hotoro ya ce babu sabani tsakanin Sanata Kwankwaso da Abba Gida Gida.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng