'Akwai Kwankwaso': Omokri Ya Jero Kusoshi a Siyasar Najeriya da Suka Kayar da Atiku a 2023

'Akwai Kwankwaso': Omokri Ya Jero Kusoshi a Siyasar Najeriya da Suka Kayar da Atiku a 2023

  • Reno Omokri ya caccaki Atiku Abubakar kan zargin an yi masa magudi a zaben 2023 da aka gudanar a Najeriya
  • Omokri ya ce rashin hadin kai ne ya kayar da Atiku tun da a 2019 ma bai samu nasara da ake hade a jam'iyyar PDP
  • Ya ce fitar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da kuma Nyesom Wike da sauran gwamnonin G5 su ne sanadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi magana kan zaben 2023 da aka gudanar.

Reno Omokri ya ce Atiku Abubakar bai ci zaɓen ba kuma ba a yi masa zalunci ba kamar yadda yake fada.

Kara karanta wannan

"Ban faɗi zaɓen 2023 ba," Atiku Ya Fallasa Yadda Tinubu Ya Masa Karfa-Ƙarfa

An fallasa wadanda suka kayar da Atiku a zaben 2023
Reno Omokri ya zargi Kwankwaso da Obi da Wike da kayar da Atiku Abubakar a zaben 2023. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Reno Omokri.
Asali: Facebook

Atiku ya yi ikirarin lashe zaben 2023

Omokri ya yi martanin ne ga Atiku a yau Talata 5 ga watan Nuwambar 2024 a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan korafin dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar kan zaben da aka gudanar.

Atiku ya yi ikirarin cewa shi ya yi nasara a zaben amma aka yi masa murdiya aka kwace masa mulki.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya fadi haka inda yake kushe tsare-tsaren shugaba Bola Tinubu a Najeriya.

Sai dai Omokri wanda ya goyi bayan Atiku a 2023 ya ce rikicin PDP ne ya kayar da shi a zaɓen.

Ya bayyana yadda Rabiu Kwankwaso da Peter Obi da kuma Nyesom Wike suka kifar da Atiku a zaɓen.

Omokri ya fadi yadda ta kaya a zaben 2023

Kara karanta wannan

2027: Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya faɗi ma'anar sunan 'T-Pain' da ake kiran Tinubu

"Na goyi bayan Atiku a 2023, faduwa ya yi zabe babu wanda ya yi masa kwace, zai yi wahala PDP ta lashe zaben 2023 tun da a 2019 da suka hada kai ba su kada APC ba."
"Mun samu kuri'u miliyan 11 a 2019, Peter Obi ya fita a 2022 da kusan kuri'u miliyan biyu, gwamnonin G5 sun fita a lokacin."
"Ga Kwankwaso ya tafi shi ma da kuri'u miliyan biyu, idan ka cire yankin Obi da Kano da Oyo da Benue da Rivers kusan miliyan shida kenan da Atiku ya samu a 2023, mun fadi ne saboda rashin hadin kai."

- Reno Omokri

APC ta yi martani ga Atiku Abubakar

Kun ji cewa Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi martani ga kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar bisa tsare-tsarenta.

Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya yi magana a sanarwar da ya fitar a farkon makon nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.