PDP Ta Fadi Kullin da Zai Kori APC daga Fagen Siyasa bayan Zaben 2027
- Jam’iyyar adawa ta PDP ta caccaki salon mulkin gwamnatin APC da a cewarta ya jefa jama’a a cikin yunwa, talauci da rashin tsaro
- Kakakin PDP, Debo Ologunagba ne ya yi martanin bayan APC ta musanta cewa ita ce ke da hannu a rikicin cikin gida da ya addabe ta
- Ya kara da cewa yanzu yan Najeriya sun yi hankali, kuma babu wanda zai sake zabar APC a zaben 2027 da dukkanin jam’iyyu ke hari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Jam’iyyar PDP ta bayyana shirin yan kasa na tabbatar da korar APC daga fagen siyasar Najeriya bayan babban zaben 2027 mai da ke tafe.
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da kakakin PDP na kasa Debo Ologunagba ranar Litinin, inda ya zargi APC da rashin gaskiya da mayar da komai siyasa.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa PDP ta zargi APC da zagin yan Najeriya da ke da karfin gwiwar bayyana ra’ayinsu a kan yadda gwamnati ke tafiyar da kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“An daina zaben jam'iyyar APC:” PDP
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta caccaki yadda gwamnatin APC ke dura a kan mutanen kasar nan idan aka yi adawa da ita.
Kakakin PDP, Ologunagba ya kara da cewa yan kasa sun farga daga karairayin da APC ke yi masu, kuma akwai tabbacin babu mai sake zabar ta a 2027.
PDP ta caccaki gwamnatin APC
Jam’iyyar PDP ta soki yadda gwamnatin Bola Tinubu ta zuba idanu yan kasar su ka fada a cikin mawuyacin hali.
PDP ta lissafa wasu daga cikin matsalolin da kasar ke fama da su da cewa sun hada da yunwa, rashin tsaro da talauci.
Jam'iyyar APC ta yi wa PDP martani
A wani labarin kun ji cewa jam’iyya mai mulki ta APC ta barranta kanta da zargin da PDP ke yi na cewa ta na hura mata wutar rikici domin hana zaman lafiya a tsakanin ‘ya’yanta a fadin kasa.
Gwamnan Oyo, Seyi Makinde ne dai ya yi zargin cewa APC ce ke jefa rikici a PDP yayin wani taro a birnin Ibadan tare da ba 'yan jam’iyyarsa shawara da su hade kansu domin yakar hakan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng