Kwankwasiyya Ta Yi Martani ga Yan Majalisun da Su Ka Bar Tafiyar Kwankwaso
- Kungiyar siyasar Kwankwasiyya a Kano ta yi martini kan ficewa da yan majalisu biyu na jam’iyyar NNPP su ka yi daga cikinta
- Dan majalisar tarayya Alhassan Rurum da takwaransa mai wakiltar Dala, Aliyu Sani Madakin Gini sun fice daga Kwankwasiyya
- Amma shugaban kungiyar siyasar na Kano, Dr. Musa Gambo Hamisu Dan Zaki ya shaidawa Legit dama ba yan Kwankwasiya ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kungiyar Kwankwasiyya a Kano ta yi martini kan ficewa da wasu jiga-jigan NNPP su ka ce sun yi daga tafiyar saboda wasu dalilai.
Shugaban kungiyar kwankwasiyya reshen jihar Kano, Dr Musa Gambo Hamisu Danzaki ya ce kamata ya yi su bar NNPP gaba daya domin da ita da Kwankwasiyya duka daya ce.
A hirarsa da Legit, Dr Musa Gambo Hamisu Danzaki ya ce babu inda ba a samun matsala irin wannan, saboda haka ficewarsu ba zai taba muhibbar Kwankwasiyya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwasiyya: An zargi ‘yan NNPP da butulci
Kungiyar Kwankwasiyya ta zargi dan majalisar tarayya mai wakilar Rano/Kibiya/Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum da dan majalisar tarayya mai wakilar Dala, Aliyu Sani Madakin Gini da butulci.
"Tun daga kan madaki da shi Rurum, dukkaninsu idan ki ka cire Kwankwasiyya a rayuwarsu, Wallahi babu su a siyasance. Kwankwasiyya ita ta yi masu riga , ita ta yi masu wando dukansu."
"Shi wancan yana yawon hauragiyarsa a Legas aka dauko shi aka ba shi takara majalisa a shekarar 2011 kuma ya ci, shi ma wancan ya na yawonsa aka dauko shi aka ba shi takarar majalisar wakilai a 2011 kuma ya ci,”
- Dr. Musa Hamisu Danzaki
Kwankwasiyya ta nemi ‘yan NNPP su bar jam’iyyar
Shugaban kungiyar Kwankwasiyya reshen Kano ya shawarci Kabiru Alhassan Rurum da Aliyu Sani Madakin Gini da su gaggauta ficewa daga cikin jam’iyyar NNPP.
"Kuma shi wannan shi ya fara yakarmu, duk wata balahira da wani abu da ya faru a lokacin Ganduje shi wannan mutumin Rurum shi ya fara hada ta."
Yan majalisu sun fice daga Kwankwasiyya
A wani labarin kun ji cewa wasu yan majalisun NNPP guda biyu sun fice daga tafiyar Kwankwasiyya wanda ake hasashen zai jawo koma baya ga Kwankwasiyya a siyasar Kano.
Alasan Rurum da Aliyu Madakin Gini sun bayyana ficewarsu daga tafiyar Kwankwasiyya a lokuta mabanbanta, guda daga cikinsu ya ce babu komai a kungiyar siyasar sai cin amana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng