2027: APC Ta yi Magana kan Saka Hannu wajen Rikita Jam'iyyar PDP

2027: APC Ta yi Magana kan Saka Hannu wajen Rikita Jam'iyyar PDP

  • APC ta yi martani kan zargin cewa ita ta hura wutar rikici da ya rikita jam'iyyar PDP ta ɓangarori da dama a Najeriya
  • An ruwaito cewa gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya yi zargin cewa APC ce ke jefa rikici a PDP yayin wani taro a birnin Ibadan
  • A cikin martanin da APC ta yi, ta ce gwamnan Oyo na shirin neman takara a zaben 2027 shi ya sa ya gagara natsuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta wanke kanta daga zargin cewa ita ce ta hura wutar rikici a cikin jam'iyyar PDP.

A karon farko, gwamnan Oyo, Seyi Makinde ne ya yi zargin cewa jam'iyyar APC ce ta kunna rikici a cikin PDP.

Kara karanta wannan

APC ta mayar da martani ga gwamna kan shirinsa na neman kujerar Tinubu a 2027

Ganduje
APC ta ce yi martani ga gwamnan Oyo. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa sakataren yada labaran APC, Felix Morka ne ya yi martani ga Seyi Makinde.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Morka: 'APC ba ta jawo rikicin PDP ba'

Sakataren yada labaran APC, Felix Morka ya ce ya kamata gwamnan Oyo ya daina zarginsu da hura wutar rikici a PDP.

Morka ya bayyana cewa babu ruwan jam'iyyar APC a kan rikicin cikin gida da PDP ke fama da shi musamman a kwanan nan.

Jam'iyyar APC ta ba gwamnan Oyo shawara

The Cable ta wallafa cewa APC ta ce maimakon zarginta, ya kamata Seyi Makinde ya mayar da hankali wajen yin aiki a jihar Oyo.

Jam'iyyar ta ce babban abin da ake bukata wajen Seyi Makinde shi ne kyautatawa talakawan jihar Oyo ba zargin wata jami'yya ba.

APC ba ta hangen nasarar PDP a 2027

Kara karanta wannan

'2027 fada ne tsakanin APC da yan Najeriya': Gwamna ya fadi abin da zai faru a zaɓe

APC ta ce duk da cewa Seyi Makinde yana da yancin tsayawa takara a 2027 amma zargin APC ba zai taimaka masa da komai ba.

Felix Morka ya kuma kara da cewa Seyi Makinde ba zai iya sauya ra'ayin masu zabe ba ko a jihar Oyo balle a fadin Najeriya.

Sakataren yada labaran APC ya jaddada cewa Bola Tinubu ya kawo tsare tsare da za su kai Najeriya gaba wanda ba za a buƙaci dawowar PDP ba.

Jam'iyyar PDP ta samu matsala a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa rikicin PDP a Kano ya ɗauki wani salo bayan ɓangaren Ibrahim Al'amin Little da Sadiq Aminu Wali sun ja daga.

A zantawarsa da manema labarai, Ibrahim Al'amin Little ya zargi tsohon gwamna Kano Malam Ibrahim Shekarau da raba PDP mai adawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng