NNPP: Majalisar Kano Ta Rabu 2, Ɓangaren Abba da Kwankwaso?

NNPP: Majalisar Kano Ta Rabu 2, Ɓangaren Abba da Kwankwaso?

  • Majalisar dokokin jihar Kano ta yi bayani kan cewa yan jam'iyyar NNPP sun rabu gida biyu saboda fitowar salon 'Abba tsaya da kafarka'
  • Shugaban masu rinjaye a majalisar, Hon. Lawan Hussaini ya yi bayani filla filla kan hakikanin abin da ke faruwa a kwanan nan a NNPP
  • Hon. Lawan Hussaini ya bayyana yadda yan majalisar NNPP suka dauki Abba Kabir Yusuf da kuma Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano, Lawan Hussaini ya yi bayani kan zargin rabuwar kai a tsakanin yan NNPP.

Hon. Lawan Hussaini ya bayyana cewa babu wata magana kan rabuwar kai a tsakanin yan Kwankwasiyya a majalisar Kano.

Kara karanta wannan

Hadimin Abba ya fadi abin da ke tsakanin gwamnan Kano da Kwankwaso

Lawan Hussaini
Majalisar Kano ta musa samuwar rabuwar kai a tsakanin yan NNPP. Hoto: Hon. Lawan Hussain
Asali: Facebook

Shugaban masu rinjaye a majalisar ya yi bayani ne a wata hirar kai tsaye da ya yi da Radiyon Freedom a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPP: 'Yan majalisar Kano sun rabu 2?

Hon. Lawan Hussaini ya bayyana cewa har yanzu babu wata ɓaraka a tsakanin yan majalisun NNPP a majalisar dokokin jihar Kano.

Shugaban masu rinjayen ya ce har yanzu a hade suke waje daya suna masu biyayya ga Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabi'u Kwankwaso.

Maganar Abba tsaya da kafarka a majalisa

Hon. Lawan Hussaini ya tabbatar da cewa su ba su da wata masaniya a kan masu da'awar Abba tsaya da kafarka a majalisa.

A cewarsa, wasu mutane ne aka ɗauki nauyinsu daga Abuja domin su kawo rikici a tsakanin yan NNPP.

Dan majalisar ya kuma kara da cewa duk wanda ya dauko kwangilar, a kwana a tashi zai ji kunya a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa ya yi rashin hadimi, wani ɗan sanda ya rasu

Har yanzu Abba na girmama Kwankwaso

Hon. Lawan Hussaini ya bayyana cewa su abin da suka sani shi ne har yanzu Abba Kabir Yusuf yana girmama Rabi'u Kwankwaso.

Ya kuma kara da cewa shi ma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Kwankwaso yana ba Abba Kabir girma a matsayinsa na gwamna.

Abba ya samu sabani da Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa an samu rahoto da ke nuna cewa an samu baraka tsakanin Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabi'u Kwankwaso.

An ruwaito cewa lamarin har ya kai ga Abba Kabir Yusuf ya daina daga wayar Sanata Kwankwaso kuma ya ki ganawa da shi a wani taro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng