Hadimin Abba Ya Fadi Abin da ke Tsakanin Gwamnan Kano da Kwankwaso
- Hadimin gwamnan jihar Kano ta karyata rade radin da ke cewa an samu baraka mai zurfi tsakanin Rabiu Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf
- Wasu rahotanni a baya bayan nan na ganin gwamnan Kano ya fara amsa kiran 'Abba tsaya da kafarka' wajen bijirewa Sanata Rabi'u Kwankwaso
- Amma tuni gwamnatin Kano ta yi martani a kan hakan, ta bayyana cewa bau wata baraka a tsakanin Abba Kabir Yusuf da Madugun Kwankwasiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan labarin bullar baraka tsakanin jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da gwamna Abba Kabir Yusuf.
Rahotanni da su ke yawo a kafafen yada labarai sun bayyana cewa baraka mai kamari ta bulla tsakanin jagororin biyu a Kano.
A martanin gwamnatin da hadimin Abba Kabir Yusuf kan kafafen sada zumunta, Salisu Yahaya Hotoro ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce babu gaskiya a cikin labarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Babu baraka tsakanin Abba da Kwankwaso" - Hotoro
Hadimin gwamna ya karyata labarin da ke cewa an samu sabani tsakanin jagoran tafiyar Kwanwkasiyya na kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf.
Sanarwar da hadimin gwamna Abba Gida Gida kan kafafen sada zumunta, Salisu Yahaya Hotoro ya fitar ta ce akwai alaka mai kyau tsakanin Kwankwaso da gwamnan.
"Abba na mutunta Kwankwaso:" Gwamnatin Kano
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa har yau, gwamna ya na ganin girman Sanata Kwankwaso a matsayin uban siyasa kuma mai bayar da shawarwari na gari.
Gwamnatin ta bukaci jama'a su yi watsi da labarin samun bullar baraka tsakanin jagororin biyu yayin da gwamnan ke kokarin mulkin jihar Kano domin samar da romon dimukuradiyya.
Gwamna Abba ya bijirewa Kwankwaso?
A baya kun ji cewa ana zargin rikici tsakanin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da jagoran Kwankwasiyya kuma Ubangidan gwamnan, Sanata Rabi'u Kwankwaso ya yi kamari.
Ana rade-radin gwamna Abba Kabir Yusuf ya amsa kiran 'Abba tsaya da kafarka,' domin ya daina amsa kiran Madugun Kwankwasiyya saboda samun sabani da rikicin siyasar jihar Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng