Nasarawa: APC Ta Lashe Kujeru 13 na Ciyamomi, Ta Fadi a Wasu Kujerun Kansiloli

Nasarawa: APC Ta Lashe Kujeru 13 na Ciyamomi, Ta Fadi a Wasu Kujerun Kansiloli

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Nasarawa, ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar
  • Shugaban hukumar NASIEC, Barista Ayuba Wandai ya bayyana cewa jam'iyyar APC ce ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 13
  • Hakazalika, Barista Wandai ya ce APC ta lashe mafi rinjayen kujerun kansilolin jihar a zaben da ya ce an gudanar cikin lumana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Jam’iyyar APC mai mulki a Nasarawa, ta lashe dukkanin kujeru 13 na shugabannnin kananan hukumomin jihar.

Hakazalika, jam'iyyar ta APC ta lashe mafi rinjayen kujerun kansiloli a zaben kananan hukumomin jihar da aka gudanar ranar Asabar.

Jam'iyyar APC ta lashe zaben ciyamomi a jihar Nasarawa
Nasarawa: APC ta lashe kujeru 13 na ciyamomi. Hoto: @NasarawaGovt
Asali: Facebook

Barista Ayuba Usman Wandai, shugaban hukumar zabe ta jihar Nasarawa (NASIEC) ya bayyana sakamakon zaben a birnin Lafiya, inji rahoton New Telegraph.

Kara karanta wannan

Abia: Jam'iyya mai mulki ta barar, bakin jam'iyyu sun lashe zaben kananan hukumomi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta ki shiga zaben ciyamomin Nasarawa

An rahoto cewa jam'iyyun siyasa tara ne suka shiga cikin wannan zabe, bayan da PDP ta nesanta kanta daga shiga zaben kananan hukumomin.

Jam'iyyar adawa ta PDP dai ta yi zargin cewa ba za a yi adalci a wajen gudanar da zaben ba don haka ba za ta wahalar da kanta wajen shiga ba.

A yayin da ya ke sanar da sakamakon zaben, Barista Ayuba ya ce jam'iyyar APC ce ta samu mafi rinjayen kuri'un da aka kada a zaben.

Nasarawa: APC ta lashe zaben ciyamomi

ThisDay ta rahoto Barista Ayuba na cewa APC ce ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi kuma jam'iyyar ce ta lashe mafi rinjayen kujerun kansiloli.

Shugaban hukumar zabe ta NASIEC, ya tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe yayin da ya kuma jinjinawa al'ummar jihar kan hadin kan da suka bayar.

Kara karanta wannan

Yadda Hadiza Bala Usman ta samu wuka da nama wajen yanka ministocin Tinubu

Shugaban ya kuma yabawa masu ruwa da tsaki, jami'an tsaro da kungiyoyin sa ido da kuma kafafen yada labarai kan irin gudumawar da suka bayar wajen samun nasarar zaben.

APC ta lashe zaben ciyamomin Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar APC ta lashe zabe a dukkanin kujerun shugabannin kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.

Jam'iyyar APC ta kuma lashe kujerun kansiloli 255 a zaben ciyamomin da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kaduna (KAD-SIECOM) ta gudanar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.