Rikicin NNPP Ya Kara Zafi bayan 'Yan Majalisa 2 Sun Fice daga Tafiyar Kwankwasiyya
- Tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso ta samu koma baya a jihar Kano
- Wasu ƴan majalisar wakilai guda biyu na jam'iyyar NNPP sun sanar da ficewarsu daga tafiyar Kwankwasiyya
- Ɗaya daga cikinsu ya bayyana cewa tafiyar Kwankwasiyya babu komai a cikinta face ƙarya, cin amana da yaudara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Ƴan majalisar wakilai biyu daga jihar Kano, na jam'iyyar NNPP sun bayyana ficewa daga tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Aliyu Sani Madakin Gini (Dala) da Alhassan Rurum (Rano/Kibiya/Bunkure) sun tabbatar da cewa ba za su ci gaba da zama cikin Kwankwasiyya ba.
Ƴan majalisar NNPP sun bar Kwankwasiyya
Alhassan Rurum, wanda tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano ne ya bayyana ficewar sa daga Kwankwasiyya a wata gajeriyar tattaunawa ta wayar tarho da jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, bai bayar da wasu takamaiman dalilan da ya sa ya yanke wannan shawarar ba sakamakon yankewar da kiran ya yi.
Meyasa suka fice daga Kwankwasiyya
Ana ganin ficewar Alhassan Rurum na da alaƙa da rikicinsa da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, musamman biyo bayan rusa masarautu biyar da ta yi.
A nasa ɓangaren, Aliyu Madakin Gini wanda shi ne mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai ya fito fili ya nesanta kansa da Kwankwasiyya yayin da yake jawabi ga al’ummar mazaɓarsa a Kano ranar Lahadi.
“Daga yau a shaida, ni Aliyu Sani Madakin Gini na daina harkar Kwankwasiyya."
"Wannan harka idan bauta ake yi, mun bauta mata, amma an ce ba mu da amfani, an ce ba mu da mutane, an ce mu tsallaka titi, to ba titi ba mun hau sama, mun yi sama."
"Ba mu shakkar kowa, ba mu tsoron kowa. Wallahi wanda bai sani ba ya sani, babu wanda ni ba zan iya tararsa gaba da gaba ba dukkan Kwankwasiyya daga sama har ƙasa."
"Na faɗa zan ƙara faɗa, Kwankwasiyya daga sama har ƙasa ƙarya ce, Kwankwasiyya yaudara ce, Kwankwasiyya cin amana ce. Wallahi duk wanda bai san wannan ba zai sani."
Aliyu Sani Madakin Gini ya kuma ba Gwamna Abba Kabir Yusuf shawara kan ya tsaya da ƙafarsa domin akwai shirin da ake ƙulla masa.
Sabon shugaban NNPP ya bayyana a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa rikici ya kara kunno kai a jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano yayin da aka samu bayyanar sabon shugaba a cikinta.
A ranar Talata, 15 ga watan Oktoba ɗaya daga cikin ƴaƴan NNPP a jihar, Dalhatu Shehu ya bayyana kansa a matsayin sabo kuma halastaccen shugaban jam'iyya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng