'2027 Fada ne Tsakanin APC da Yan Najeriya': Gwamna Ya Fadi Abin da Zai Faru a Zaɓe

'2027 Fada ne Tsakanin APC da Yan Najeriya': Gwamna Ya Fadi Abin da Zai Faru a Zaɓe

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya caccaki tsarin jam'iyyar APC wurin kakabawa al'umma halin kunci
  • Makinde ya bayyana cewa zaben Najeriya a 2027 ya rage tsakanin jam'iyyar APC da kuma al'ummar kasar
  • Ya ce gwamnatin APC ta rikita kasar da talauci da rashin iya mulki tun bayan karbar ragamar Najeriya a zaben 2015

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya sake magana kan zaben 2027 da jam'iyyar APC a Najeriya.

Makinde ya bayyana damuwa kan yadda jam'iyyar ta galabaitar da al'ummar Najeriya da rashin iya mulki.

Gwamna ya soki tsarin tsarin mulkin APC a Najeriya
Gwamna Seyi Makinde ya ce zaben 2027 fada ne tsakanin APC da yan Najeriya. Hoto: Seyi Makinde, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Gwamna ya magantu kan zaben APC a 2027

Gwamna Makinde ya bayyana haka yayin kaddamar da sabon ofishin sakatariyar PDP a Ibadan, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

APC ta mayar da martani ga gwamna kan shirinsa na neman kujerar Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makinde ya ce zaben 2027 zai zamo zakaran gwajin dafi ne tsakanin APC da kuma yan Najeriya duba da halin da suka jefa al'umma a ciki.

Gwamnan ya caccaki tsare-tsaren mulkin Bola Ahmed Tinubu inda ya ce ta yaudari yan Najeriya, kamar yadda rahoton Punch ta ruwaito.

'Zabe ya rage tsakanin APC da yan Najeriya' - Makinde

"APC ta dade tana mulkin kasar nan inda ta yaudari al'ummar Najeriya da kuma tsunduma su a halin kunci."
"Yanzu ya ragewa yan kasar a zaben 2027 su kifar da APC ko kuma su cigaba da barinsu a kan mulki."
"A 2027, ba zabe ne tsakanin PDP da APC ba, illa zabe tsakanin APC mai mulki da kuma makomar al'ummar Najeriya."

- Seyi Makinde

Legit Hausa ta yi magana da masoyin PDP

Kara karanta wannan

Gwamna ya kakaba harajin N40,000 kan mafi ƙarancin albashi? Fintiri ya yi martani

Kwamred Abubakar Aliyu ya ce abin da yake ransa Gwamna Makinde ya fada a yau inda ya ce APC ta gama musu aiki.

Aliyu ya ce zai yi wahala mai hankali ya sake zaben APC a 2027 ko da kuwa yana ci a jikinta idan yana da tausayi.

Sai dai ya koka kan yadda ake saurin yaudarar yan Arewa a lokacin zabe inda ya ce abin takaici ne amma yana fatan Allah ya tsare faruwar hakan.

Makinde ya magantu kan kalubalantar Tinubu

Kun ji cewa yayin da ake hasashen yana neman shugabancin Najeriya, Gwamna Seyi Makinde ya yi martani kan haka jita-jitar da ake yaɗawa.

Gwamna Makinde na jihar Oyo ya bayyana haka ne yayin da ake jita-jitar yana neman kalubalantar Bola Tinubu a zaben shekarar 2027.

Makinde ya ce a yanzu ya yi girman da zai bayyana muradinsa kan lamarin da ya shafi siyasa idan yana so ba tare da tsoron kowa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.