'Ban Samu Komai a Gwamnati ba': Kanin Tsohon Gwamna Ya Kwance Masa Zani a Kasuwa

'Ban Samu Komai a Gwamnati ba': Kanin Tsohon Gwamna Ya Kwance Masa Zani a Kasuwa

  • Kanin tsohon gwamnan Ekiti, Isaac Fayose ya sake kunto wata ta'asa inda ya ce yayansa Ayodele Fayose bai taba ba shi kwangila ba
  • Isaac ya musanta zargin da ake yaɗawa cewa ya yi kudi ne lokacin da Ayodele Fayose ke mukin jihar Ekiti
  • Daga bisani, Isaac ya ware N50m a matsayin tukuici ga duk wanda ya nuna kwangilar da ya samu a gwamnatin Fayose

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ekiti - Kanin tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya kalubanci masu cewa an bashi kwangila a lokacin mulkin yayansa.

Isaac Fayose ya sanya tukuicin N50m ga duk wanda ya nuna wani kwanigla guda daya da aka ba shi a lokacin mulkin Ayodele Fayose a jihar.

Kara karanta wannan

Limamin masallacin Abuja, Maqary ya yi magana mai zafi sakamakon kama 'yan yara

Dan uwan tsohon gwamna ya kalubanci al'umma kan zargin samun kwangila a mulkin Fayose
Kanin tsohon gwamna, Ayodele Fayose ya ƙaryata samun kwangila a mulkin yayansa. Hoto: Isaac Fayose.
Asali: Facebook

Isaac ya sanya tukuicin N50m kan kwangila

Isaac ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin Instagram a yau Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Isaac ya ce duk wani cigaban da ya samu daga Allah ne ba wata harkar kasuwanci da dan uwansa ba.

Ya koka kan yadda ake yawan cewa yana kashe kudin jihar Ekiti inda ya ko kwabo bai samu ba a mulkin.

Har ila yau, Isaac ya ce shi ɗan kasuwa ne kuma ya yi imani da harkokin da yake yi suna ba shi abin da yake so.

Kanin gwamna ya musanta karbar kwangila

"Kuna cewa ina kashe kudin Ekiti, yayana bai ba ni kwangila ko guda daya ba lokacin da yake mulki, duk wanda ya fadi inda aka ba ni kwangila zan ba shi N50m."

Kara karanta wannan

Gwamna ya kakaba harajin N40,000 kan mafi ƙarancin albashi? Fintiri ya yi martani

"Duk karya ce, ban samu ko kwangila daya ba, ya kamata ya gada, ni ba dan kwangila ba ne, ni dan kasuwa ne."

- Isaac Fayose

Isaac Fayose ya nada kansa shugaban PDP

Kun ji cewa rigimar jam'iyyar PDP ta sauya salo bayan kanin tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya ayyana kansa shugabanta.

Kanin tsohon gwamnan Ekiti mai suna Isaac Fayose ya ce daga yau shi ne shugabanta duk wanda ba yarda ba ya je kotu.

Hakan ya biyo bayan rikicin da ya barke a PDP da ke neman raba ta gida biyu bayan tsaginta ya dakatar da shugabanta, Umar Damagum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.