Majalisar Dokoki Ta Dakatar da Shugaban Karamar Hukuma kan Wani Bidiyon Rashin Ɗa'a
- Majalisar dokokin jihar Oyo ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Oyo ta Gabas, Olusola Oluokun kan wani bidiyo da ya jawo ce-ce-ku-ce
- Bidiyon dai ya nuna shugaban karamar hukumar yana cin abinci kusan tsirara, sannan yana zagin wasu masu adawa da ubangidansa na siyasa
- Kakakin majalisar dokokin jihar Oyo ya ce ba za su lamunci irin wannan halayya ba domin ba ta dace da zababben shugaban ƙaramar hukuma ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Majalisar dokokin jihar Oyo ta dakatar da shugaban karamar hukumar Oyo ta gabas, Olusola Oluokun.
Majalisar ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar ne kan wani faifan bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya, wanda ya haifar da zazzafar muhawara.
Me shugaban ƙaramar hukumar ya yi a bidiyo?
Kamar yadda Daily Trust ta kawo, bidiyon ya nuna Oluokun yana cin abinci kusan tsirara, sannan yana yabawa wani jigon siyasa da ya taimaka masa ya zama ciyaman.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sannan kuma a bidiyon an ji yana zagin masu adawa da wannan ɗan siyasa watau ubangidansa, ana ganin hakan bai dace ba a matsayinsa na zaɓaɓɓen ciyaman.
Majalisar dokoki ta ɗauki mataki
Majalisar dokokin ta kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin, sannan ta umarci mataimakin ciyaman ya kula da ayyukan ofishin Oluokun na wani dan lokaci.
Majalisar ta yi Allah-wadai da lamarin, inda ta bayyana shi a matsayin wanda bai dace da zababben shugaban karamar hukuma ba.
Shugaban majalisar dokokin jihar Oyo, Hon. Adebo Ogundoyin ya bayyana cewa majalisar ba za ta lamurci irin waɗannan halayen na rashin ɗa'a ba, Tribune ta rahoto.
Ya ce wannan matakin da majalisa ta ɗauka cikin gaggawa wata alama ce da ke nuna a shirye take ta kare duk wani muƙamin gwamnati daga gurbatattun mutane.
Majalisa ta fara shirin raba jihar Oyo
A wani rahoton, an ji cewa majalisar wakilai ta fara yunkurin kirkiro sabuwar jiha a Najeriya inda take shirin raba Oyo zuwa jihohi biyu, kamar Ibadan da Oyo.
Akeem Adeyemi da wasu ‘yan majalisu ne suka dauki nauyin kudirin, sun nemi a kafa jihar Ibadan, da Ibadan a matsayin babban birni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng