'Shi ne Gatansa': Hadimin Tinubu Ya Fadi Wanda Ya Yi Sanadin Samun Mulkin Buhari
- Minista a mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ƙaryata rade-radin cewa ya ci amanar Bola Tinubu
- Sunday Dare ya ce bai taba cin amanar Tinubu ba inda ya ce duk muƙamin da ya samu sai da sahalewar shugaban kasar
- Dare wanda yanzu Tinubu ya nada a matsayin hadiminsa ya fadi rawar da mai gidansa ya taka a lokacin zaben 2015
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari ya fadi wanda ya taimaka tsohon shugaban kasar.
Sunday Dare ya ce idan ba domin goyon bayan Bola Tinubu ba da Buhari bai samu mulki ba a zaben shekarar 2015.
Dare ya fadi gatan da Tinubu ya yi masa
Sunday Dare ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Alhamis 31 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabon hadimin na Tinubu ya ce duk wani mukami da ya samu sai da sahalewar Tinubu tun farko kuma a kowane mataki.
Tsohon Ministan ya ƙaryata jita-jitar cewa ya ci amanar Tinubu inda ya fake tare da Muhammadu Buhari domin samun muƙami.
Rawar da Tinubu ya taka a zaben Buhari
"A dalilin menene zan ci amanar Tinubu? Dwani mukami da ka ga na samu da sahalewarsa ne."
"Ban san a ina kuka samu wannan labari ba, amma ba ni da matsala da Tinubu, kafin zuwa na hukumar NCC shi ne ya yi komai, lokacin da Buhari ya ba ni Minista duk da saninsa kuma abu ne wanda za ka bautawa kasa."
"Ka duba rawar da Tinubu ya taka a jam'iyyar APC wurin hadaka, idan ba domin shugaban ba a wancan lokaci da Buhari bai zama shugaban kasa ba."
- Sunday Dare
2015: Jonathan ya fadi halin da ya shiga
Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya tuno lokacin da ya fadi zaben da aka yi a 2015 a hannun Muhammadu Buhari.
Jonathan ya bayyana irin mummunan yanayi da ya shiga kan faduwa zaben, ya ce ba abu ba ne mai sauki a rayuwa a rasa mulki.
Tsohon shugaban kasar ya ce ba zai taba mantawa da marigayi Raymond Dokpesi ba kan yadda ya tsaya tare da shi a wancan lokaci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng