Fubara Ya Fadi Wanda Ya Saba Alkawari bayan Tinubu Ya yi Sulhu tsakaninsa da Wike

Fubara Ya Fadi Wanda Ya Saba Alkawari bayan Tinubu Ya yi Sulhu tsakaninsa da Wike

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya yi magana kan zaman sulhu da shugaban Bola Tinubu ya yi tsakaninsa da Nyesom Wike
  • Siminalayi Fubara ya zargi Nyesom Wike da karya sharudan da aka gindaya yayin zaman sulhun da suka yi a fadar shugaban kasa
  • A watan Disambar 2023 Fubara da Wike suka rattaba hannu kan takardar sulhu mai sharuda takwas domin kawo zaman lafiya a Rivers

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya yi magana a kan sulhun da Bola Tinubu ya yi a tsakaninsa da Nyesom Wike.

Gwamna Fubara ya yi zargin cewa bayan sun saka hannu kan takardar sulhun, yan bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike sun saba alkawari.

Kara karanta wannan

'Muna tausaya muku': Gwamnonin APC sun magantu kan halin kunci, sun ba da tabbaci

Fubara
Fubara ya yi magana kan sulhunsa da Wike. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Nyesom Ezonwo Wike|Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Jaridar the Cable ta wallafa cewa gwamna Siminalayi Fubara ya fadi dalilin amincewa da yin sulhun a karon farko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya yi wa Fubara da Wike sulhu

Bayan samun rikicin siyasa tsakanin gwamnan Rivers da ministan Abuja, Tinubu ya tsoma baki a 2023.

Shugaba Bola Tinubu ya yi sulhu a tsakanin yan siyasar inda ake tsammanin lamarin zai kawo ƙarshen rikicin Rivers.

Gwamna Fubara ya zargi Wike da karya doka

Vanguard ta wallafa cewa gwamna Siminalayi Fubara ya ce bayan an yi sulhu a tsakaninsu, Nyesom Wike bai bi sharudan sulhun ba.

Fubara ya ce sun cika alkawarin soke ƙarar da suka kai Wike kotu amma shi ya ki ya cire ƙarar da ya kai su gaban alkali.

Dalilin Fubara na yarda da sulhu

Gwamna Siminalayi Fubara ya ce son samar da zaman lafiya a Rivers ne ya sanya shi amincewa da sulhun da Bola Tinubu ya yi musu.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun bukaci Sanatocin Arewa su yi watsi da wata buƙatar Tinubu

"Saboda mu mutane ne masu son zaman lafiya, idan akwai wani abu da ya sanya mu yarda da sulhun to shi ne son zaman lafiya.
Sai dai duk da haka, wadansu da suke tunanin sun fi mu wayo sun yaudare mu bayan sulhun."

- Siminalayi Fubara

Kotu ta hana turawa Rivers kudi

A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta zartar da hukunci kan neman hana sakarwa jihar Rivers kuɗi duk wata.

Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Joyce Abdulmalik ta hana gwamnatin tarayya sakarwa jihar Rivers kasonta daga asusun FAAC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng