Tsagin Ganduje a Kano Sun Bayyana Wanda Suke Son Ya Karɓi Shugabancin APC
- Magoya bayan Abdullahi Ganduje a Kano sun bayyana Ibrahim Gwarzo a matsayin ɗan takararsu na shugabancin APC ta jiha
- Mai magana da yawun wata kungiyar masu kishin APC ya ce suna goyon bayan Ibrahim Ɗan'azumi Gwarzo ne saboda gogewarsa
- Kungiyar magoya bayan dai na ƙarƙashin tsohon sakataren gwamnatin jihar a lokacin mulkin Ganduje, Alhaji Abubakar Alhaji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Magoya bayan shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje sun fara faɗi tashi kan wanda suke son ya gaji kujerar shugaban jam'iyyar a Kano.
Ƴaƴan APC da ke goyon bayan Ganduje sun zaɓi Ibrahim Dan’azumi Gwarzo a matsayin ɗan takararsu na shugaban jam'iyyar reshen jihar Kano.
Magoya bayan Ganduje a karkashin kungiyar masu kishin APC, sun bayyana hakan ne jiya Laraba a wani taron manema labarai, Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar dai na karkashin jagorancin Abubakar Alhaji wanda shi ne sakataren gwamnatin jihar a lokacin Ganduje na gwamna.
Magoya bayan Ganduje sun fara tuntuɓar manya
Da yake yi wa manema labarai jawabi a jiya, kakakin kungiyar, Saleh Adamu Kwaru, ya ce sun sanar da waɗanda ya kamata game da shawarar da suka yanke.
A cewarsa, sun sanar da Ganduje, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin da mai bada shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu kan wanda suke so a kujerar shugaban APC ta Kano.
Ya ce sun kuma sanar da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari da dan takarar gwamnan Kano na APC a zaben 2023, Nasiru Gawuna.
Ganduje: Ina makomar Abdullahi Abbas?
Duk da sun bayyana wanda suke so tun kafin taron APC da ake sa ran yi a shekara mai zuwa, kakakin ƙungiyar ya ce ba su adawa da shugaban yanzu, Abdullahi Abbas.
Saleh Adamu ya ce sun zaɓi Gwarzo ne saboda APC a Kano na bukatar mutum tsayayye kuma kwararre mai kishin kasa wanda zai iya tara wa jam’iyyar goyon baya.
Ya kara da cewa dan takararsu ya karbi lambar yabon jajirtaccen mutum 2022 daga gidauniyar Gani Fawehinmi.
Barau ya ce APC za ta karɓi Kano
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Barau I. Jibrin ya ce jam'iyyar APC na shirin karɓe mulkin jihar Kano a babban zaɓe mai zuwa a 2027.
Mataimakin shugaban majalisar ya faɗi haka ne a lokacin da ake tantance sabon ƙaramin ministan gidaje da raya birane.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng