Sanata Ya Tada Hankalin Gwamna Abba, Ya ce Jam'iyyar APC Za Ta Kwace Kano a 2027
- Sanata Barau I. Jibrin ya ce jam'iyyar APC na shirin karɓe mulkin jihar Kano a babban zaɓe mai zuwa a 2027
- Mataimakin shugaban majalisar ya faɗi haka ne a lokacin da ake tantance sabon ƙaramin ministan gidaje da raya birane
- Yusuf Ata ya bayyana a gaban majalisar dattawa ne domin tantance shi da tabbatar da naɗin da aka yi masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce jam’iyyar APC za ta karbe mulkin jihar Kano a babban zabe mai zuwa.
Sanata Barau ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana kan nadin Yusuf Abdullahi Ata daga Kano a matsayin minista a zauren majalisar dattawa.
Sanata Barau ya yi magana kan naɗin ɗan Kano
Leadership ta tattaro cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Yusuf Abdullahi a matsayin karamin minista a ma'aikatar gidaje da raya birane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yau Laraba Yusufa Ata ya bayyana a gaban majalisar dattawa domin tantance shi da kuma yiwuwar tabbatar da naɗinsa ko akasin haka, in ji Punch.
"Jam'iyyar APC za ta karɓi Kano" - Barau
Da yake tsokaci kan sabon ministan, Sanata Barau mai wakiltar Kano ta Arewa ya ce:
"Mai girma shugaba, ba zan cika ku da surutu ba amma wannan mutumin da ke gaban ku (Yusuf Ata) babban ɗan siyasa ne shiyasa ɗaya daga cikinmu a nan ya ce ana masa barazana."
"Mutum ne mai gogewa da kwarewa wanda al'umma suke kauna, da zaran an tabbatar da shi a matsayin minista, babu shakka APC za ta karɓe Kano."
Tasirin Kano a siyasar Najeriya
Kano da ke Arewa maso Yamma, jiha mafi girma a Arewa kuma ta biyu a fadin Najeriya mai yawan al'umma sama da miliyan 15. Jihar tana da tasiri a siyasar Najeriya.
A halin yanzu Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ke mulki a jihar bayan karewar wa'adin Abdullahi Umar Ganduje.
Talakawa sun fi yawa a Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa sabon ministan jin ƙai da yaki da talauci, Nentawe Yilwatda, ya ce talakawa sun fi yawa a Arewacin Najeriya fiye da kudu.
Da yake jawabi a majalisar dattawa, Yilwatda ya ce kaso 65% na talakawa ƴan Arewa ne don haka ya kamata a rika ware masu kaso mai tsoka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng