Rikicin PDP Ya Ki Karewa a Kano, An Yi wa 'Yan Bangaren Shekarau Taron Dangi

Rikicin PDP Ya Ki Karewa a Kano, An Yi wa 'Yan Bangaren Shekarau Taron Dangi

  • Rikicin PDP a Kano ya ɗauki wani salo bayan ɓangaren Ibrahim Al'amin Little da Sadiq Aminu Wali sun ja daga
  • A zantawarsa da manema labarai, Ibrahim Al'amin Little ya zargi tsohon gwamna Ibrahim Shekarau da raba PDP
  • A tattaunawarsa da Legit, sabon shugaban PDP, Hon. Yusuf Ado Kibiya ya ce ana ƙoƙarin ɗinke barakar da ta kunno kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kwanaki kaɗan da zaɓen sababbin shugabanni a jam'iyyar PDP a Kano, rikici ya kunno cikinta inda aka samu masu adawa da shugabancin Yusuf Ado Kibiya.

Tsagin PDP da ke mubaya'a ga Ibrahim Al'amin Little da Sadiq Wali ya sha alwashin dawo da martabar jam'iyyar a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sanata ya tada hankalin Gwamna Abba, ya ce jam'iyyar APC za ta ƙwace Kano a 2027

Little
Rikici ya kunno kai PDP a Kano Hoto: Abubakar Lamido
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta tattaro tsagin Al'amin Little na zargin tsagin tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau da raba kan PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An raba PDP gida 2 a Kano" - Al'amin Little

Tsagin Al'amin Little na PDP a Kano ya zargi tsohon gwamna, Malam Ibrahim Shekarau da raba kan jam'iyyar gida biyu.

Ibrahim Al'amin Little ya bayyana haka ne yayin ganawa da yan jam'iyyar daga kananan hukumomin jihar Kano 44 da kuma manema labarai.

Rikicin PDP: Tsagin Shekarau ya yi martani

Sabon shugaban PDP a Kano, kuma tsohon kwamishina, Yusuf Ado Kibiya ya ce su na sane da koken wasu daga cikin yan jam'iyyar.

A tattaunawarsa da Legit ta wayar tarho, ya tabbatar da cewa da tsaginsu da na Al'amin Little duk tafiya ɗaya ce, kuma za a kawo karshen koken da su ke da shi.

Kara karanta wannan

Tarkon Ganduje ya yi kamu, dan Majalisar Zamfara ya fadi dalilin dawowa APC

Hon Yusuf Ado Kibiya ya ce samun irin wannan matsala ba sabon abu ba ne a kowace jam'iyya, kuma hakan ba shi ne zai raba kawunan yan PDP a Kano ba.

Jigon PDP a Kano ya dauko sabuwar tafiya

A baya kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, kuma guda daga ƙusoshin jam'iyyar PDP, Malam Ibrahim Shekarau ya jagoranci tawagar sabuwar ƙungiyar siyasa a Arewa.

A ziyarar da tawagar tsohon gwamnan ta kai wa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjon, Sanata Shekarau ya ce tafiyar za ta zaburar da yan Arewa kan shugabanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.