Tarkon Ganduje Ya Yi Kamu, Dan Majalisar Zamfara Ya Fadi Dalilin Dawowa APC

Tarkon Ganduje Ya Yi Kamu, Dan Majalisar Zamfara Ya Fadi Dalilin Dawowa APC

  • Jam'iyyar APC a Najeriya ta yi babban kamu bayan dan Majalisar Tarayya mai ci ya yi fatali da PDP a jihar Zamfara
  • Hon. Abubakar Gumi da ke wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum a jihar ya koma APC ne saboda rikice-rikicen da ke PDP
  • Shugaban Majalisar Tarayya, Hon. Tajudden Abbas shi ya tabbatar da haka a yau Laraba 30 ga watan Oktoban 2024 a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Dan Majalisar Tarayya mai ci ya watsar da PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Hon. Abubakar Gumi shi ke wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Dan majalisar kano ya jero illolin rashin wuta a arewa, ya ga gazawar gwamnati

Dan Majalisar Tarayya ta watsar da PDP zuwa APC
Dan Majalisar Tarayya, Hon. Abubakar Gumi ya sauya sheka daga PDP zuwa APC a jihar Zamfara. Hoto: All Progressives Congress, Hon. Sulaiman Abubakar Gumi.
Asali: Facebook

Hon. Gumi ya bar PDP zuwa jam'iyyar APC

Shugaban Majalisar, Hon. Tajudden Abbas shi ya tabbatar da haka a zaman Majalisar, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Gumi ya ce ya sauya sheka ne saboda rigimar cikin gida da ke addabar PDP a mazabarsa da ke jihar Zamfara, TheCable ta ruwaito.

"Hon. Gumi ya ce akwai shugabannin jam'iyyar guda biyu a mazabarsa, da kuma rikici ta ko ina inda ya ce jam'iyyar ba ta da tsari ko kadan."

- Hon. Tajudden Abbas

An kalubalanci shugaban majalisa kan sauya shekar

Wannan sauya shekar na zuwa ne makwanni biyu bayan nada Hon. Gumi, shugaban kwamitin hukumar raya yankin Arewa maso Yamma a Majalisar.

Sai dai shugaban marasa rinjaye a Majalisar, Hon. Kingsley China ya ci gyaran shugaban Majalisar kan yadda ya yi magana game da sauya shekar.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar PDP, jam'iyyar APC ta dakatar da tsohon gwamna

Hon. Chinda ya ce ya kamata Hon. Tajudden ya bi tsarin doka kamar yadda ya kamata a matsayinsa na shugaban majalisar wakilai.

Yan APC sun gargadi Tinubu bayan korar Minista

Ƙun ji cewa wata kungiyar matasan APC a jihar Kano ta nuna damuwa kan sallamar tsohon karamin Ministan gidaje da raya birane.

Kungiyar ta ce tabbas duk wanda ya ba Bola Tinubu shawarar sallamar Abdullahi Gwarzo ya yaudari shugaban kasar.

Hakan ya biyo bayan korar wasu daga cikin ministoci da Bola Tinubu ya yi a cikin makon da ya gabata bayan korafin yan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.