Ana Tsaka da Rigimar PDP, Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Tsohon Gwamna
- Rikicin jam'iyyar APC mai ci ya sake sauya salo bayan dakatar da tsohon gwamnan jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola
- Jam'iyyar reshen jihar ta ce tana zargin tsohon Ministan da kawo rudani da farraka APC a Osun domin biyan bukatarsa
- Wannan na zuwa ne bayan mika takardar korafi kan tsohon gwamnan ga shugaban APC ta kasa, Abdullahi Ganduje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - Jam'iyyar APC a Osun ta fatattaki tsohon gwamnan jihar, Ogbeni Rauf Aregbesola daga cikinta.
Jam'iyyar mai adawa a jihar ta dauki matakin ne bayan zargin Aregbesola da cin dunduniyarta da neman raba ta gida biyu.
Musabbabin dakatar da tsohon gwamna daga APC
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka turawa shugaban jam'iyyar ta kasa, Abdullahi Ganduje, cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar ta ce Aregbesola ya rikita APC tare da kawo baraka a cikinta wurin samar da bangarori biyu da suke gaba da juna.
Ta ce hakan wani nufi na jawowa APC nakasu musamman a wannan lokaci da ake ciki na siyasa a jihar Osun.
Jam'iyyar ta ce Aregbesola ya kawo rigimar da kuma lalata hadin kan APC wanda ya yi matukar tasiri, Punch ta ruwaito.
Osun: Shirin kawo gyara da APC ke yi
Wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen jam'iyyar wurin kakkabe dukan wadanda suke yi mata zangon-kasa komai girmansu a APC.
Sai dai har zuwa wannan lokaci, ɓangaren Aregbesola bai yi martani ba kan dakatarwar da aka yi wa tsohon Ministan a mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
APC ta cire Aregbesola daga jagororin jam'iyya
A baya, kun ji cewa jam’iyyar APC reshen jihar Osun ta kai karar Rauf Aregbesola, tsohon gwamnan jihar ga kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa.
APC ta zargi Aregbesola, wanda tsohon ministan Najeriya ne da kafa kungiyoyi da ke zagon kasa ga jam'iyyar a jihar.
Shugaban APC na jihar, Tajudeen Lawal ya gargadi 'yayan jam'iyyar da su kiyayi alaka da Aregbesola kasancewar yanzu ba su tare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng