An Samu Karin Bayani bayan Dakatar da Tantace Sababbin Ministocin Tinubu a Yau

An Samu Karin Bayani bayan Dakatar da Tantace Sababbin Ministocin Tinubu a Yau

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta tabbatar da cewa an dage shirin tantance sababbin Ministoci da shugaban kasa ya nada
  • Fadar shugaban kasar ta ce an dage tantancewar domin ba sababbin Ministocin damar kammala hada takardunsu
  • Hakan ya biyo bayan shirin tantance sababbin Ministocin a yau Talata 29 ga watan Oktoban 2024 da muke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - A yau Talata 29 ga watan Oktoban 2024 Majalisar Tarayya ta shirya tantance sababbin Ministoci da Bola Tinubu ya nada.

Sai dai Gwamnatin Bola Tinubu ta sanar da cewa an dage tantance Ministocin a yau Talata da aka shirya a Abuja.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta waiwayi sababbin ministocin da Tinubu ya naɗa, bayanai sun fito

An dage tantance sababbin Ministoci da ake shirin yi a Abuja
Gwamnatin Bola Tinubu ta sanar da fasa tantance sababbin Ministoci. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

Tinubu ya yi garambawul a gwamnatinsa

Hadimin Bola Tinubu a bangaren Majalisar, Sanata Basheer Lado shi ya tabbatar da haka a yau Talata, cewar rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya yi garambawul a gwamnatinsa inda ya watsa Ministoci guda biyar.

Bayan sallamar Ministocin, Tinubu ya kuma yi sauye-sauye, ya hade wasu ma'aikatu tare da rushe wasu.

Daga bisani ya nada sababbin Ministoci har guda bakwai wadanda aka yi niyyar tantance su a yau Talata 29 ga watan Oktoban 2024.

Musabbabin dage tantance Ministocin Tinubu

Sanata Lado ya ce an dage tantance sababbin Ministocin ne zuwa gobe Laraba 30 ga watan Oktoban 2024.

Lado ya ce an dauki matakin ne domin ba sababbin Ministocin damar kammala shirye-shiryensu kafin tantancewar.

Sanatan ya ce a yanzu an dage tantancewar zuwa gobe Laraba a dakin Majalisar da misalin karfe 12.00 na rana.

Kara karanta wannan

Kusa a PDP ya soki Tinubu kan kyale Mawatalle a mukaminsa, ya fadi illar haka

Barin Matawalle: Jigon PDP ya soki Tinubu

Kun ji cewa jigon jam'iyyar PDP a jihar Kogi ya caccaki Shugaba Bola Tinubu kan garambawul da ya yi a gwamnatinsa inda ya ce an bar baya da kura.

Kusa a PDP, Usman Okai Austin ya ce abin takaici ne yadda Tinubu ya bar karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle a mukaminsa duk da zarge-zarge a kansa.

Hakan na zuwa ne bayan Tinubu ya yi garambawul a gwamnatinsa inda wasu ke korafi kan rashin sallamar Matawalle da kuma babban Ministan tsaro, Badaru Abubakar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.