Kano: Hadimin Gwamna Ya Sauya Sheka a Shirin Kifar da Abba a 2027
- Sanata Barau Jibrin ya karbi da dama daga cikin magoya bayan jam'iyyar NNPP mai mulki a ƙananan hukumomin Kano
- Daga cikin wadanda suka fice zuwa APC akwai tsohon hadimin gwamna Abba Kabir Yusuf a bangaren shari'a da wasu mutanensa
- Sanata Jibrin ya bayyana yadda za su cigaba da tafiya tare da wadanda suka sauya shekar domin kwato Kano daga mulkin NNPP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karbi yan APC da suka sauya sheka zuwa APC.
Tsohon hadimin gwamnan Kano, Barista Nura Abdullahi Bagwai na cikin waɗanda suka sauya shekar.
Legit ta samo bayanai kan sauya sheƙar ne a cikin wani sako da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon hadimin Abba ya bar NNPP
Tsohon hadimin Abba Kabir a harkar shari'a, Barista Nura Abdullahi ya fice daga NNPP zuwa APC.
Barista Nura Abdullahi ya jagoranci tarin yan NNPP ne zuwa ofishin Sanata Barau domin sauya sheka a Abuja.
Shugabannin NNPP sun koma APC
A daya bangaren, shugabannin wata kungiyar NNPP a mazabu 11 na karamar hukumar Dawakin Tofa sun koma APC.
Malamin makaranta kuma ɗan siyasa, Shehu Hussaini Abdul ne ya jagoranci yan APC zuwa NNPP a Dawakin Tofa.
Wadanda suka sauya shekar sun ce amincewa da yadda Barau Jibrin ke kawo cigaba ne ya saka su daukar matakin.
Bayanin Sanata Barau Jibrin
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa dama NNPP ba ta samu karɓuwa a Kano ta Arewa ba kuma sun kyauta da suka sauya shekar.
Sanata Barau ya jaddada musu cewa za su yi aiki tare domin ceto jihar Kano da kuma inganta rayuwar al'umma.
Yan Kannywood sun sauya sheka daga NNPP
A wani rahoton, kun ji cewa a kwanan nan ana kara samun yan jam'iyyar NNPP A jihar Kano na cigaba da sauya sheka zuwa jami'yyar APC.
A wannan karon, wasu fitattun jaruman Kannywood sun kara ficewa daga tafiyar gwamna Abba Kabir Yusuf suka koma APC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng