Shugaba Bola Tinubu Ya Naɗa Kansa a Matsayin Minista? Gaskiya Ta Bayyana

Shugaba Bola Tinubu Ya Naɗa Kansa a Matsayin Minista? Gaskiya Ta Bayyana

  • Fadar shugaban ƙasa ta musanta zargin cewa Shugaba ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ministan man fetur a Najeriya
  • Hadimin shugaban kasa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya ce ko da wasa Tinubu bai taɓa naɗa kansa a matsayin minista mai ba
  • Onanuga ya ƙara da cewa shugaban ƙasa na sane da halin kuncin da ƴan Najeriya ke ciki kuma ya na kokarin yaye duk wata damuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta musanta raɗe-radin da ke yawo cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa kansa a matsayin ministan man fetur.

Babban mashawarcin shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ranar Lahadin da ta gabata.

Kara karanta wannan

Betta Edu ta faɗi abin da ta hango a mulkin Tinubu bayan an koreta daga minista

Bola Tinubu.
Fadar shugaban kasa ta musanta zargin Tinubu ne ministan man fetur Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Onanuga ya musanta jita-jitar ne a wata hira da gidan talabijin na Channels tv cikin shirin siyasa a yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ke rike da ministan man fetur?

Da yake amsa tambayoyi kan matsayin shugaban kasa a bangaren man fetur, Onanuga ya fayyace cewa Tinubu bai taba keɓewa kansa mukamin ministan man fetur ba.

Bayo Onanuga ya ce:

"Shugaban ƙasa bai taɓa kiran kansa da matsayin ministan man fetur ba, soshiyal midiya ce ta naɗa shi a wannan muƙamin.
"Muna da ministoci biyu a ɓangaren mai, ɗaya an ware shi a fannin harkokin gas, ɓangare mai muhimmanci da aka yi watsi da shi.

Onanuga ya kuma jaddada kudirin Tinubu na bunƙasa ɓangaren gas, yana mai kafa hujja da kalaman tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, wanda ya ce ya yi kuskure a mulkinsa.

"Tinubu na sane da halin da ake ciki" - Onanuga

Kara karanta wannan

Betta Edu: Fadar shugaban kasa ta fadi matsayin ministar da Tinubu ya dakatar

Hadimin shugaban ƙasar ya musanta zargin da ƴan Najeriya ke yi cewa shugaba Tinubu ba ya tausaya masu kan matsin tattalin arzikin da suke fuskanta.

A cewarsa, Tinubu na sane ɗa wahalar da ake sha a Najeriya kuma ya himmatu wajen warware dukkan kalubalen da ake fama da su a ƙasar nan, Tribune ta kawo labarin.

'Gwamnatin Tinubu za ta kawo sauyi'

A wani rahoton kuma Betta Edu ta bayyana cewa tana da ƙwarin guiwar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai kawo sauyi a Najeriya.

Tsohuwar ministan jin kai ta buƙaci ƴan Najeriya su ƙara hakuri, duk wannan matsin zai zama tarihi nan ba da daɗewa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262