Kwankwaso Ya Ba 'Yan Arewa Mafita kan Zaben 2027 da Ke Tafe

Kwankwaso Ya Ba 'Yan Arewa Mafita kan Zaben 2027 da Ke Tafe

  • Ƙusa a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya ba ƴan Arewa mafita kan zaɓen shekarar 2027 da ke tafe
  • Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya buƙaci ƴan Arewa da su marawa Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima baya a 2027
  • Jigon na APC ya bayyana cewa goyon bayan na su ne zai sanya mulki ya dawo yankin Arewa a shekarar 2031

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wani ƙusa a jam’iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso ya jaddada cewa ya fi kyau Arewa ta goyi bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu a zaɓen 2027 domin mulki ya koma yankin a 2031.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma jaddada bukatar ƴan siyasa masu kishin kasa su yi watsi da yunƙurin da wasu ke yi na ɓata gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

Ganduje ya sake cika baki, ya fadi jihar da APC za ta kwace

Kwankwaso ya bukaci 'yan Arewa su zabi Tinubu
Musa Kwankwaso ya bukaci 'yan Arewa su marawa Tinubu/Shettima baya a 2027 Hoto: @DOlusegun, @KashimSM
Asali: Facebook

Jigon na APC ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Kano a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya ba ƴan Arewa shawara

Musa Kwankwaso ya bayyana cewa idan wani mutum ɗan Kudu bayan Tinubu ya ci zaɓe a 2027, hakan na nufin Arewa sai ta sake jira tsawon shekara takwas kafin mulki ya dawo yankin.

Ya yi kira ga ƴan siyasan Arewa da ka da su yarda da kiraye-kirayen da wasu ke yi kan wani ɗan takara ya fito daga yankin Kudu a zaɓe shi a zaɓen 2027.

"Mu a Arewa dole ne mu haɗa kai mu tabbatar an sake zaɓar Tinubu da Shetima a zaɓen 2027."
"Zai fi kyau ƴan Arewa domin kare muradin Arewa su goyi bayan tikitin Shugaba Tinubu/Shettima a 2027 wanda hakan zai sa mulki ya dawo yankin a 2031."

Kara karanta wannan

Matawalle: Dalilin Tinubu na barin minista da ake zargi da "daukar nauyin 'yan bindiga"

"Duk ɗan Kudu da wasu ƴan Arewa ke tunanin goyon baya a 2027 to tabbas zai so ya yi shekara takwas, ma'ana mulki zai iya dawowa Arewa a 2035."

- Musa Iliyasu Kwankwaso

Kwankwaso ya magantu kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigon jam’iyyar APC a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya gargaɗi ƴan Najeriya da su daina siyasantar da al’amuran tsaro.

Kwankwaso ya bayyana cewa siyasantar da al’amuran tsaro na kawo cikas ga ci gaban yaƙi da rashin tsaro da gwamnatin tarayya ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng