Kusa a PDP ya Soki Tinubu kan Kyale Mawatalle a Mukaminsa, Ya Fadi Illar Haka

Kusa a PDP ya Soki Tinubu kan Kyale Mawatalle a Mukaminsa, Ya Fadi Illar Haka

  • Jigon jam'iyyar PDP a jihar Kogi ya caccaki Shugaba Bola Tinubu kan garambawul da ya yi a gwamnatinsa
  • Usman Okai Austin ya ce abin takaici ne yadda Tinubu ya bar karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle a mukaminsa
  • Hakan na zuwa ne bayan Tinubu ya yi garambawul a gwamnatinsa inda wasu ke korafi kan rashin sallamar Matawalle

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon dan takara a Majalisar Tarayya a PDP ya caccaki Bola Tinubu game da garambawul.

Austin Okai da ya yi takara a zaɓen 2023 ya koka kan yadda aka bar karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle kan muƙaminsa.

An soki Tinubu bayan kwale Matawalle a mukaminsa
Jigon PDP a Najeriya ya caccaki Bola Tinubu game da barin Bello Matawalle a mukaminsa. Hoto: Usman Okai Austin, @Bellomatawalle1, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Dan PDP ya bukaci a kori Bello Matawalle

Kara karanta wannan

Ana cikin halin kunci, Tinubu ya ware gwamna 1 a Najeriya, ya yaba masa

Jigon PDP a jihar Kogi ya bayana haka ne yayin hira ta musamman da Legit a yau Lahadi 27 ga watan Oktoban 2024 da muke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okai ya caccaki Tinubu inda ya ce ya kamata a ce an sallami Matawalle saboda zargin alakar da yake da shi da yan bindiga.

Ya ce barin Matawalle a mukaminsa na karamin Ministan tsaro zai kawo cikas ga lamarin tsaron Najeriya baki daya.

Ministoci: Jigon PDP ya soki nadin Tinubu

"Matakin barin Ministocin tsaro guda biyu akwai alamun tambayoyi duba da abubuwa da suke faruwa, misali Matawalle ana zargi yana da alaka da yan ta'adda."
"Har ila yau, hukumar EFCC na zargin Matawalle da wasu almundahana na makudan kudi wanda hakan bai dace ba."
"Sannan nadin wasu Ministoci ya tabbatar da nuna wariya na jam'iyya wanda ya kamata a yi duba wurin kwarewar mutum."

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya buƙaci Shugaba Tinubu ya ƙara korar wasu ministoci daga aiki

- Usman Okai Austin

Ndume ya bukaci Tinubu ya sake garambawul

Kun ji cewa Sanata Mohammed Ali Ndume ya yabawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa garambawul din da ya yi a gwamnatinsa.

Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu ya buƙaci Tinubu ya sake haska majalisar zartaswa domin akwai sauran ministocin da ya kamata a kora.

Ya kuma baiwa shugaban ƙasar shawarar ya haɗa taron tattalin arziki domin lalubo mafita da wannan halin da ƙasa ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.