Gwamna Abba Ya Yi Magana kan Zaben Kano, Ya Tura Sako ga Bangaren Shari'a

Gwamna Abba Ya Yi Magana kan Zaben Kano, Ya Tura Sako ga Bangaren Shari'a

  • Gwamnan jihar Kano ya nuna gamsuwarsa kan yadda hukumar zaɓe ta KANSIEC ta gudanar da zaɓen ciyamomi a Kano
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zaɓen shi ne mafi inganci da aka taɓa gudanarwa a tarihin Kano
  • Ya yabawa shugaban hukumar KANSIEC da ma'aikatanta kan yadda suka tabbatar an gudanar da sahihin zaɓe a ƙananan hukumomi 44 na jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

Gwamna Abba ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali a faɗin ƙananan hukumomin jihar 44.

Gwamna Abba ya magantu kan zaben Kano
Gwamna Abba ya ce an yi sahihin zabe a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamna Abba ya kaɗa ƙuri'arsa

Jaridar Daily Trust ta ce da yake magana bayan kaɗa ƙuri’arsa a ƙaramar hukumar Gwale, gwamnan ya bayyana jin daɗinsa kan goyon bayan da sauran shugabannin hukumomin zaɓe na jihohi suka ba da ta hanyar sanya ido a zaɓen.

Kara karanta wannan

Halin da mutane ke ciki a Kano yayin da zaɓen ƙananan hukumomi ya kankama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya bayyana cewa zaɓen da aka gudanar a mazaɓu 484 a faɗin ƙananan hukumomi 44, shi ne mafi inganci a tarihin Kano.

Gwamnan ya yabawa shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) da ma’aikatanta kan yadda suka tabbatar da gudanar da sahihin zaɓe a Kano.

Gwamna Abba ya tura saƙo ga ɓangaren shari'a

"Ina kira ga ɓangaren shari’a da su ci gaba da kasancewa ƴan ba ruwanmu idan ana maganar zaɓe. Ba abu ne mai kyau a ce ɓangaren shari'ar mu ya riƙa sanya siyasa a harkokinsa."
"Duk da cewa gwamnatin jihar Kano ce kaɗai gwamnatin da ta hau mulki a ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, bai kamata a tsoratar da mu ba, mutanen Kano mutane ne masu son zaman lafiya amma idan aka kaisu bango za su iya maida martani."

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya sa doka a Kano ana dab da fara zaɓen ƙananan hukumomi

"Mun ga abin da ya faru a Rivers, don haka mun ɗauki matakan da suka dace don ganin ba a samu irin wannan lamarin a Kano ba."

Gwamna Abba Kabir

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma bukaci ƴan adawa da su amince da shan kaye, saboda irin goyon bayan da jam’iyyarsa ke da shi na masu kaɗa ƙuri’a.

Gwamna Abba ya sa doka

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon sa'o'i 18 daga karfe 12:00 na dare zuwa karfe 6:00 na yammacin ranar Asabar, 26 ga watan Oktoban 2024.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar zaɓen jihar watau KANSIEC ke gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ranar, 26 ga watan Oktoba, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng