Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Soki Sakacin APC a Kano, Ya Fadi Kuskuren da Ake Yi
- Tsohon kwamishina a Kano, Mu'az Magaji ya caccaki tsarin yadda jam'iyyar APC ke neman mulki a jihar
- Magaji ya ce kwata-kwata bai goyon bayan yadda jam'iyyar ke dogara da karfin gwamnati daga sama
- Ya ce idan za ta sake lale kawai ta yi domin a fito a nemi al'umma a zabe da kuma mutunta yan jam'iyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Yayin da ake cigaba da zaben kananan hukumomi a Kano, tsohon kwamishina, Mu'az Magaji ya ba jam'iyyar APC shawara
Tsohon kwamishinan ayyuka a mulkin Abdullahi Ganduje ya gargadi jam'iyyar kan cigaba da dogara da karfin Gwamnatin Tarayya.
Kusa a APC ya soki tsarinta a Kano
Mu'az Magaji ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a yau Asabar 26 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Magaji ya ce kwata-kwata hanyar da APC ke bi a siyasar Kano kuskure ne dole ta sake lale domin dawo da martabarta.
Tsohon kwamishinan ya ce ya kamata APC ta nemi al'umma a zabe ba wai yanke hukuncin zaben daga sama ba.
Kano: Mu'az Magaji ya ba APC shawara
"Za mu tafka kuskure babba a APC idan mu ka cigaba da dogara da karfin Gwamnatinmu a sama don samun nasarar siyasa a Kano."
"Irin wannan ne yasa aka kada mu a 2023, siyasa daban gwamnati daban, sai mun sake lale a Kano."
"Ni bana goyon bayan a rika yanke hukuncin zabe da juya siyasar Kano daga sama, a bari kowa ya nemi mutane, a daraja yan jamiyya, a yi bayanin abinda za a aiwatar wa mutane har su amsa mana, mu karbe abinda suka karba da kyar."
- Mu'az Magaji
Babu jami'an tsaro a zaben Kano
Mun baku labarin cewa ana cigaba da gudanar da zaben kananan hukumomi a Kano ba tare da jami'an tsaro ba a mafi yawan wurare.
Mafi yawan mazabu babu jami'an tsaro sai dai yan banga rike da sanda da adduna da kuma yan KAROTA da ke kula da hanyoyi.
Asali: Legit.ng