Kananan Hukumomi: Halin da Ake Ciki a Kano da Aka Rasa Jami'an Tsaro a Wasu Wurare

Kananan Hukumomi: Halin da Ake Ciki a Kano da Aka Rasa Jami'an Tsaro a Wasu Wurare

  • Ana cigaba da kada kuri'a a zaben kananan hukumomi da ake yi a jihar Kano a yau Asabar 26 ga watan Oktoban 2024
  • Sai dai mafi yawan wurare yan banga ne ke ba da tsaro rike da sanduna da kuma adduna da suka kera
  • Hakan ya biyo bayan fara kada kuri'a a zaben bayan kotu ta ba hukumar KANSIEC damar cigaba da zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Halin da ake ciki a jihar Kano game da tsaro yayin da ake ci gaba da zaben kananan hukumomi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mafi yawan mazabu babu jam'ian tsaro sai dai yan banga da ke ba al'umma tsaro.

Kara karanta wannan

Kano: Sarki Sanusi II ya magantu kan zaben kananan hukumomi, ya tura sako

Halin da ake ciki a Kano kan zaben kananan hukumomi
Yadda ake cigaba da zaben kananan hukumomi a jihar Kano. Hoto: Legit.
Asali: Original

Kotu ta ba hukumar zaben Kano dama

Wakilin Channels TV ya tabbatar da cewa yan banga ne da sanduna da kuma adduna ke ba mutane tsaro a mafi yawan mazabu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan hukuncin kotu kan zaben kananan hukumomi da ta ba hukumar KANSIEC damar gudanar da zaɓen.

Hukuncin na zuwa ne bayan kalubalantar zaben kananan hukumomin da jam'iyyun siyasa suka yi a jihar.

Mai Shari'a, Sanusi Ma’aji shi ya yanke hukuncin inda ya ce KANSIEC tana da ikon yin haka a kundin tsarin mulki.

Ma'aji ya ce kundin tsarin mulki ya ba hukumar KANSIEC damar gudanarwa da kula da zaben har zuwa karshe.

Kano: Yadda yan banga ke ba da tsaro

A halin yanzu, ana cigaba da zaben kananan hukumomi a Kano ba tare da wani tashin hankali ba.

Kara karanta wannan

Kalubale 4 da kananan hukumomi 774 za su fuskanta bayan samun gashin Kai

Daga cikin hukumomi masu ba da tsaro a zaben akwai KAROTA da ke kula da kare hatsura a hanyoyi a jihar.

Yan Kano sun yiwa hukumomi biyayya

Kun ji cewa Yayin da zaɓe ya kankama a jihar Kano, rahotanni sun nuna mutane sun yi biyayya ga umarnin taƙaita zirga-zirga.

A yau Asabar 26 ga watan Oktoba aka tsara yin zaɓen kananan hukumomi a jihar Kano duk da umarnin kotun tarayya.

Bayanai sun nuna cewa galibin shagunan ƴan kasuwa a kulle suke, tituna kuma babu yawan ababen hawa a cikin kwaryar birnkn Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.