'Mene Ya Kai Shi Masallaci': An Soki Akpabio da Aka Gano Shi da Tinubu a Sallar Juma'a

'Mene Ya Kai Shi Masallaci': An Soki Akpabio da Aka Gano Shi da Tinubu a Sallar Juma'a

  • Yan Najeriya sun yi ta korafi bayan ganin shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a cikin masallacin Juma'a
  • Wasu da suka tofa albarkacin bakinsu sun fara tambayar mene dalilin zuwan Akpabio cikin masallaci a matsayinsa na Kirista
  • Hakan ya biyo bayan haduwar jiga-jigan Najeriya daga kowane da bangare da kuma jam'iyyu a cikin masallacin Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya hadu da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a masallacin Abuja.

Wannan haduwa ita ce ta farko tun bayan karawar da suka yi a zaben 2023 da aka gudanar a Najeriya.

An dira kan Akpabio bayan ganinsa a cikin masallaci da Tinubu
Bola Tinubu ya hadu da Atiku a masallacin Juma'a, an soki Akpabio. Hoto: Godswill Obot Akpabio, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

An soki Akpabio kan zuwa masallacin Juma'a

Kara karanta wannan

Tinubu, Ganduje sun yi kicibis da Atiku da manyan yan adawarsa a siyasa, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NTA News ta ruwaito cewa Tinubu ya hadu da Atiku ne a masallacin Abuja yayin daurin auren yar Sanata Danjuma Goje.

A cikin masallacin akwai shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio wanda ya jawo cece-kuce a ƙasa.

Yan Najeriya da dama sun soki Akpabio bayan ganinsa a masallacin Juma'a a matsayinsa na Kirista.

Martanin yan Najeriya kan shigan Akpabio masallaci

@Dr_dabo1:

"Siyasa kenan, Akpabio ya je salla masallacin Abuja, yanzu ya dawo da Alhaji Gambo Alkassim."

@RealMrF_O:

"Godswill Akpabio har masallacin Juma'a ya bi Tinubu ya zauna a gaba saboda munafurcin siyasa."

@Adeywaley_H:

"Mene Akpabio ke yi a masallacin Juma'a kuma?"

@Jidejay_:

"Don Allah mene Akpabio ke yi a cikin masallaci har da carbi a hannu?"

@AlhajiDNA:

"Babban abin da ya dame ni shi ne mene Akpabio ke yi a cikin masallaci?"

Kara karanta wannan

Jerin ministocin da Tinubu ya kora daga aiki da jihohin da suka fito a Najeriya

@Eazyy622121:

"Akpabio a cikin masallaci….. siyasa kenan babu abin da ba zaka gani ba."

Tinubu ya hadu da Atiku a masallacin Abuja

Mun baku labarin cewa an yi kicibis bayan Shugaba Bola Tinubu ya hadu da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Shugaba Tinubu ya ci karo da babban mai masa adawa a siyasa wanda ya yi takara da shi a zaben 2023 da ta gabata.

Shugaban kasar ya hadu da Atiku ne a babban masallacin birnin Tarayya da ke Abuja yayin sallar Juma'a a jiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.