Minista Ya Yi Wata Magana, Ya Roki Ƴan Najeriya Su Ci Gaba da Yi Wa Tinubu Addu'a
- Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya yi kira ga ƴan Najeriya su ci gaba da yi wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu addu'a
- Wike ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya kinkimo aiki mai girma wanda ke buƙatar addu'a domin cimma nasara
- Tsohon gwamnan ya ce gwamnatin tarayya ta himmatu wajen ganin ta dawo da fatan da mutane suka rasa a baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, a ranar Juma’a ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugaban kasa, Bola Tinubu addu’a.
Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ɗan PDP ya bayyana cewa Shugaba Tinubu na da niyya mai kyau ta inganta rayuwar ƴan Najeriya.
Ya faɗi hakan ne a wajen kaddamar da fara gina titin Arterial Road, wanda aka fi sani da Obafemi Awolowo Way, a Life Camp da ke Abuja, Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu za ta dawo da fatan mutane
Ministan ya ce gwamnatin Tinubu ta maida hankali wajen yin ayyukan da za su farfaɗo da fatan al'umma.
"Saboda haka ina son dukkanku ku ci gaba da yi wa shugaban kasa addu’a domin a karshe ya cimma burinsa, fatan da al’ummarmu ke da shi ya dawo, shi ya sa ya zo da ajendar sabunta fata."
"Burin wannan gwamnatin ta dawo da fatan da mutane suka rasa, na tabbata mutanen da ke zaune a nan sun cire rai da wannan aiki amma shugaban ƙasa ya ce ba abin da ba zai yiwu ba."
- Nyesom Wike.
Wike ya roki goyon bayan ƴan Najeriya
Ministan ya ƙara da cewa sai da shugaban ƙasa ya amince sannan aka fara dukkan ayyukan da ake yi a birnin Abuja
Wike ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya su ci gaba da goyon bayan gwamnati mai ci domin ta samu kwarin guiwar cika alƙawurran, rahoton jaridar Pulse.
Ministan Abuja ya ɗauki zafi kan zanga-zanga
A wani labarin kuma ministan Abuja, Nyesom Wike ya caccaki mazauna yankin Lugbe da ke birnin bisa zanga zangar adawa da rushe-rushensa.
Hukumar gudanarwar Abuja ta fara rushe wasu wuraren da ta ce an yi gine-gine a filayen da ta ce an mallaka ba bisa ka'ida ba
Asali: Legit.ng