Gwamna Abba Ya Sa Doka a Kano Ana Dab da Fara Zaɓen Kananan Hukumomi

Gwamna Abba Ya Sa Doka a Kano Ana Dab da Fara Zaɓen Kananan Hukumomi

  • Yayin da ake shirin zaben kananan hukumomi a jihar Kano, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga
  • Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Baba Halilu Ɗantiye ya ce dokar za ta yi aiki na tsawon sa'o'i 18 a ranar Asabar
  • Baba Ɗantiye ya roƙi mazauna Kano su bi dokar sau da ƙafa domin a samu damar gudanar da zaɓen cikin lumana da kwanciyar hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ƙano - Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon sa'o'i 18 daga karfe 12:00 na dare zuwa karfe 6:00 na yammacin ranar Asabar.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar zaɓen jihar watau KANSIEC ke shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a yau 26 ga watan Oktoba, 2024.

Kara karanta wannan

Halin da mutane ke ciki a Kano yayin da zaɓen ƙananan hukumomi ya kankama

Gwamna Abba Kabir.
Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana zirga-zirga na tsawon sa'o'i 18 Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Baba Halilu Dantiye ya fitar ranar Juma'a, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnatin ta ɗauƙi wannan matakin ne bayan zaman tattaunawa da hukumomin tsaro.

Gwamnati ya roki jama'a su bada haɗin kai

Baba Ɗantiye ta bukaci jama'a su mutunta dokar takaita zirga-zirgar kana su ba da gudummuwa bakin gwargwado wajen ganin zaɓen ya gudana yadda ya dace.

"Muna ƙara jaddada aniyarmu ta gudanar da zabe mai inganci, gaskiya, sahihanci, kuma cikin lumana," in ji shi.

Matakin dai ya shafi mutane da ababen hawa a fadin kananan hukumomi 44 da kuma gundumomi 484 na jihar Kano.

Wannan doka na zuwa ne sa'o'i kaɗan gabanin fara harkokin zaben ciyamomi da kansioli, wanda aka tsara yi yau Asabar, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Minista ta taimaka wajen samo $57.5bn domin kafa Biafara? Gaskiya ta fito

Dalilin taƙaita zirga-zirga a Kano

Kwamishinan ya ce an sa dokar ne domin tabbatar da tsaro, daƙile duk wata barazana da ka iya kawo tangarɗa, da samar da yanayi mai kyau na gudanar da sahihin zabe.

Sai dai duk da haka ya ce akwai waɗanda dokar ba zata hau kansu ba kamar malaman zaɓe, jami'an tsaro da sauran masu muhimman ayyuka.

Sanusi II ya ba mutanen Kano shawara

A wani rahoton kuma yayin da ake ƙoƙarin gudanar da zaɓen kananan hukumomi a Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II ya ba da shawarwari ga iyaye

Sarki Muhammadu Sanusi ya shawarci iyaye da su kange ƴaƴansu daga shiga rigima yayin gudanar da zaben a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262