Ciyamomin Ƙananan Hukumomi 3 a Arewa Sun Gamu da Hatsari da Babura yayin Zuwa Ofis

Ciyamomin Ƙananan Hukumomi 3 a Arewa Sun Gamu da Hatsari da Babura yayin Zuwa Ofis

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa ciyamomin kananan hukumomi uku ne suka gamu da hatsari da baburansu yayin zuwa ofis
  • An tabbatar da cewa hakan ya faru ne saboda rashin samun ababan hawa a hukumance daga gwamnatin jihar Benue
  • Hakan ya biyo bayan shigansu ofis tun a farkon watan Oktoban 2024 ba tare da motoci ba inda suka koma amfani da babura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Rashin ababan hawa ga shugabanni kananan hukumomi a jihar Benue ya jawo musu iftila'i.

Wasu shugabannin kananan hukumomi uku sun gamu da hatsari a kan baburansu yayin zuwa ofisoshinsu.

Ana fargabar ciyamomin ƙananan hukumomi sun yi hatsari da babura
Shugabannin kananan hukumomi a Benue sun gamu da hatsari a kan baburansu. Hoto: Legit.
Asali: Original

Ciyamomi sun koma hawa babura a Benue

Kara karanta wannan

Ana matsalar lantarki. 'yan Arewa sun dura kan Tinubu, sun ragargaje shi

The Guardian ta ce rashin motoci ne ya tilastawa shugabannin kananan hukumomin hawa babura domin sauke hakkokin al'umma a kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta tabbatar da cewa ciyamomin sun samu raunuka daban-daban yayin hatsarin da suka ci karo da shi, cewar rahoton Tribune.

An gano cewa tun bayan hawansu mulki a farkon watan Oktoban 2024, gwamnatin jihar ba ta ba su motoci ba makwanni uku kenan da shiga ofis.

Yadda ciyamomin ƙananan hukumomi suka samu raunuka

"Abun takaici ne tun bayan nasarar da shugabannin kananan hukumomi suka samu makwanni uku da suka wuce amma ba a ba su motocin hawa ba."
"Saboda damuwa da burin sauke nauyin da aka daura musu, ciyamomin sun koma hawa babura domin zuwa ofisoshinsu daban-daban da ke faɗin jihar."
"Daga bayanan da muke samu, a cikin wadanda suka yi hatsarin akwai wanda ya samu gurdewar kashi inda yake karbar kulawa a yanzu."

Kara karanta wannan

Nadin Minista ya jefa Tinubu a matsala, APC ta zarge shi da cin amanar jam'iyya

- Cewar wata majiya

Gwamna Alia ya dakatar da kwamishinansa

Mun baku labarin cewa gwamnan jihar Benue, Alia Hyacinth ya dakatar da wani kwamishinansa kan shiga shari'a ba tare da saninsa ba.

Alia ya dauki matakin ne kan kwamishinan shari'a, Fidelis Mynin game da korafin da ake yi kan hukumar EFCC a Najeriya.

Hakan ya biyo bayan maka hukumar EFCC da wasu gwamnoni 16 suka yi a kotu kan rashin ingancin dokar da ta samar da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.