Kano: Sarki Sanusi II Ya Magantu kan Zaben Kananan Hukumomi, Ya Tura Sako
- Ana ƙoƙarin gudanar kananan hukumomi a Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II ya ba da shawarwari ga iyaye
- Sarki Muhammadu Sanusi ya shawarci iyaye da su kange ƴaƴansu daga shiga rigima yayin gudanar da zaben a jihar
- Hakan ya biyo bayan shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi a gobe Asabar 25 ga watan Oktoban 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan zaben kananan hukumomi.
Sarki Sanusi II ya shawarci iyayen yara da matasa da su ja kunnen 'ya'yansu kan shiga rikici yayin zaɓen a jihar Kano.
Kananan hukumomi: Sanusi II ya shawarci iyaye
Vanguard ta tabbatar da cewa Sarkin ya fadi haka ne yayin ganawa da yan jaridu a yau Juma'a 25 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanusi II ya ce duk mai kaunar jihar Kano zai so a ce ta zauna lafiya ba tare da neman tashin hankali ba, cewar rahoton Punch.
"Ga mutane na yan jihar Kano, kamar yadda kuka sani a gobe Asabar za a gudanar da zaben kananan hukumomi."
- Muhammadu Sanusi II
Sarki Sanusi ya tura sako ga limamai
"Duk wadanda suke son Kano, ina da tabbacin cewa za su yarda da ni cewa babu abin da yafi zaman lafiya muhimmanci."
"Wadanda ke kawo rigima a Kano mafi yawansu makiyanta ne, za su ta da rigima kuma a ta kashe kannenmu da 'ya'yanmu."
"Ina kira ga iyaye da masu unguwanni da hakimai da kuma limamai da su ja kunnen matasa kan ta da rigima."
- Sarki Muhammadu Sanusi II
Babu APC a zaben kananan hukumomin Kano
Kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano ta ce dama a shirye ta ke wajen gudunar da zaben ciyamomi ba tare da cikas ba.
Shugaban hukumar, Farfesa Sani Malumfashi ya fadi haka jim kaɗan bayan hukuncin babbar kotun jiha da ya sahale a yi zabe.
Farfesa Sani Malumfashi ya ce amma babbar jam'iyyar adawa ta APC ta fice daga zaben duk da zama da aka yi da ita.
Asali: Legit.ng