Tinubu, Ganduje Sun Yi Kicibis da Atiku da Manyan Yan Adawarsa a Siyasa, Bayanai Sun Fito
- An yi kicibis bayan Shugaba Bola Tinubu ya hadu da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
- Shugaba Tinubu ya ci karo da babban mai masa adawa a siyasa wanda ya yi takara da shi a zaben 2023 da ta gabata
- Shugaban kasar ya hadu da Atiku ne a babban masallacin birnin Tarayya da ke Abuja yayin sallar Juma'a a yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ci karo da manyan yan adawansa a birnin Abuja.
Bola Tinubu ya yi kicibis da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a masallacin Juma'a.
Atiku ya ci karo da Tinubu a masallacin Juma'a
NTA News ta wallafa wani hoto da aka dauka bayan sallar Juma'a da aka gudanar a babban masallacin Abuja yayin auren yar Sanata Danjuma Goje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin hoton, an gano shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje yana rike da Alkur'ani mai girma a gefe.
Daga cikin wadanda suke tare a cikin masallacin akwai Gwama Bala Mohammed na jihar Bauchi wanda yake yawan sukar gwamnatin Tinubu.
Har ila yau, a can gefe, akwai tsohon gwamnan Borno kuma jigon jam'iyyar APC, Sanata Ali Modu Sherrif.
Karanta wasu labarai game da Atiku da Tinubu
- ‘Jam’iyyar Yunwa:’ Atiku Ya Fadawa Mutanen Edo Abin da Zai Faru Idan PDP Ta Ci Zabe
- Nadin Minista Ya Jefa Tinubu a Matsala, APC Ta Zarge Shi da Cin Amanar Jam'iyya
- 'Za Su Hana Tinubu Takara a 2027?’ Kusa Ya Dura kan Masu Sukar Atiku
- Bayan Kora, Tinubu Ya ba Ministoci Umarnin Rage Kashe Kudin Gwamnati
Atiku ya soki tsarin mulkin Bola Tinubu
Kun ji cewa Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu saboda matakin da ta dauka kan NLC.
Atiku Abubakar ya ce yadda gwamnatin kasar nan ke kokarin murkushe kungiyoyin kwadago na nuna tsagwaron zalunci.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kuma buga misali da yadda aka kama wani dan jarida, bayan an sake shi aka ce kuskure ne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng