"Ban da APC:" KANSIEC Ta Fadi Jam'iyyun da ke Takara a Zaben Kano

"Ban da APC:" KANSIEC Ta Fadi Jam'iyyun da ke Takara a Zaben Kano

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano ta ce dama a shirye ta ke wajen gudunar da zaben ciyamomi ba tare da cikas ba
  • Shugaban hukumar, Farfesa Sani Malumfashi ya fadi haka jim kaɗan bayan hukuncin babbar kotun jiha da ya sahale a yi zabe
  • Farfesa Sani Malumfashi ya ce amma babbar jam'iyyar adawa ta APC ta fice daga zaben duk da zama da aka yi da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Awanni bayan babbar kotun jiha ta sahalewa hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano (KANSIEC) damar gudanar da zabe, hukumar ta magantu.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kasa da awanni 24 kafin zaben Ciyamomi a jihar Kano

Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ya bayyana cewa tuni su ka kammala shirin gudanar da zabe ba tare da matsala ba.

Siyasa
APC ta fice daga zaben kananan hukumomin Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro shugaban ya dauki alkawarin tabbatar da an yi zabe a cikin gaskiya tare da adalci yayin bayyana wadanda su ka yi nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar KANSIEC ta ja kunnen masu zabe

Shugaban hukumar KANSIEC, Farfesa Sani Malumfashi ya ce ba za su lamunci gudanar da abubuwan da doka ta haramta yayin zaben kananan hukumomi a gobe ba.

Shugaban hukumar ya ce ba za su amince da sayen kuri'a ko barin yara ƙanana su yi zaɓe ko kuma ba jami'an KANSIEC cin hanci ba.

KANSIEC ta fadi jam'iyyun da ke takara

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano (KANSIEC) ta lissafa jam'iyyun da ke takara a zaben kananan hukumomin da za a gudanar a ranar 26 Oktoba, 2024.

Kara karanta wannan

"Babu wanda ya isa:" Abba ya yi martani kan hana zaben ƙananan hukumomin Kano

Farfesa Sani Malumfashi ya ce jam'iyyun da ke takara sun hada Action Alliance, ZLP, Accord, AAC, NRM da NNPP.

Malumfashi ya ce babbar jam'iyyar adawa ta APC ta fice daga takara a zaben duk da zama da aka yi da jagororinta.

Kotu ta amince KANSIEC ta yi zabe

A baya mun ruwaito cewa babbar kotun jiha karkashin Mai Shari'a Sunusi Ma'aji ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta da gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Asabar.

Wannan na zuwa bayan wata babbar kotun tarayya karkashin Simon Amobode ta haramta gudanar da zaben, tare da soke nadin shugaban hukumar, Farfesa Sani Malumfashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.