Nadin Minista Ya Jefa Tinubu a Matsala, APC Ta Zarge Shi da Cin Amanar Jam'iyyar

Nadin Minista Ya Jefa Tinubu a Matsala, APC Ta Zarge Shi da Cin Amanar Jam'iyyar

  • Shugabannin jam'iyyar APC a jihar Anambra sun kalubalanci shugaba Bola Tinubu kan nadin Bianca Odinaka Odumegu Ojukwu a matsayin Minista
  • Shugabannin sun nuna damuwa kan matakin da Tinubu ya dauka ba tare da ya nemi shawarar su ba inda suka ce hakan cin amana ne
  • Hakan ya biyo bayan sallamar wasu Ministoci guda biyar da Tinubu ya yi inda ya amince da nadin wasu mutum bakwai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - Nadin Bianca Odinaka Odumegu Ojukwu da Bola Tinubu ya yi ya bar baya da kura a jihar Anambra.

Shugabannin jam'iyyar APC a jihar sun yi fatali da matakin nadin Bianca a matsayin Minista a gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

Bayan kora, Tinubu ya ba ministoci umarnin rage kashe kudin gwamnati

APC ta caccaki Tinubu kan nadin Bianca a matsayin Minista
Jam'iyyar APC a Anambra ta soki Bola Tinubu kan nadin Bianca Ojukwu a matsayin Minista. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

APC ta zargi Tinubu da cin amanarta

Tribune ta ruwaito cewa shugabannin jam'iyyar na zargin Tinubu da cin amanar APC kan nadin Bianca a wannan matsayi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin wata ganawar gaggawa a birnin Awka, shugabannin sun ki amincewa da nadin Bianca da Tinubu ya yi.

Sun nuna damuwa kan ainihin dalilinsa na amincewa da Bianca a matsayin Minista ba tare da neman shawarar su ba, cewar rahoton Pulse.

APC ta ce Tinubu bai mutunta yan jam'iyya

Har ila yau, suka ce wannan nadin ya saba ka'ida duba da bautar da suka yi inda suka ce hakan zai kashewa sauran mambobin jam'iyyar guiwa.

"Wannan ba komai ba ne illa cin amanar jam'iyya, a wane dalili za a dauko wanda bai sha wahala ba a bar yan jam'iyya, Tinubu bai mutunta bautar da sauran mambobi suka yi."

Kara karanta wannan

Ana ta kiran a tsige shi, bayan ya sha da kyar, Minista ya yabawa matakin Tinubu

"Shin Tinubu so yake yi a samu dubban yan APC da za su koma APGA? ko dai yana yiwa APGA aiki ne a boye ba mu sani ba.?"

- Shugabannin APC a Anambra

Tinubu ya nada matar Odumegu Ojukwu Minista

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada sababbin Ministoci guda bakwai bayan sallamar wasu daga ciki da kuma yin sauye-sauye.

Tinubu ya amince da nadin matar marigayi Odumegu Ojukwu, Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu a matsayin Ministar waje.

An kuma tsohon Ministan Muhammadu Buhari, Muhammadu Maigari Dingyadi a matsayin Ministan ayyuka da kwadago.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.