Masoyan Peter Obi Sun Yi Masa Watsa Watsa a Fili a dalilin Turawa Gowon Sako
- Peter Obi ya yi amfani da shafinsa na X wajen taya Yakubu Gowon murnar cika shekara 90 a duniya
- Magoya bayan Obi musamman daga Kudu maso Ibo sun soke shi saboda bakar kiyayyarsu da Gowon
- Gowon da sojojin Najeriya sun takawa Ibo burki, yunkurin rike Najeriya ya jawo asarar rayukar jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Peter Obi ya samu karbuwa tun gabanin zaben 2019 kuma har yanzu ya na da farin jini musamman daga Kudu maso gabas.
Kaunar da ake yi wa Peter Obi ta taimaka Atiku Abubakar ya samu kuri’u masu yawa a zaben 2019 kuma LP ta ba da mamaki a 2023.
Peter Obi ya taya Yakubu Gowon murna
A makon da ya gabata Yakubu Gowon ya shekara 90 a duniya, Peter Obi ya na cikin wadanda suka taya sa murna a dandalin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da karbuwar Peter Obi a Kudu maso gabas, mutanen yankin sun fito sun yi tir da shi, har da masu cewa sun yi watsi da shi a siyasa.
Janar Yakubu Gowon yana mulki ‘yan Kudu maso gabas a karkashin Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu suka nemi suka kafa Biyafara.
An soki Peter Obi a X
Morris Monye yana cikin wadanda suka fara tir da Obi a shafin X, ya ce bai yi daidai ba.
Christopher Okenwa ya ce Obi ya fito masu a mutum, kuma a wurinsu Gowon mai laifi ne wanda ya hallaka miliyoyin mutanen Biyafara.
"Ina ganin girmanka, amma ban tare da kai. Gwamnatinsa ce dalilin cire darashin tarihi a makarantu.
"Ban kallonsa (Gowon) a matsayin shugaba."
- Chima Echefule
Wani @Bumi_Speaks ya zargi gwamnatin Gowon da kisan kare dangi, ya ce dama ya nunawa mutane Obi bai da maraba da sauran ‘yan siyasa.
Har ila yau a dandalin ne Foundational Igbo man ya ce sun yi hannun riga da Obi, a cewarsa Gowon ya kashe miliyoyin inyamurai.
Ayo Sogunro ya ce da wannan maganar, da gum kurum Peter Obi ya yi, da ya fi masa.
Tosin Olugbenga ya fadakar da mutane cewa dole a cire kiyayya, shi kuwa Prince Adeshina ya ce dama ya san za a ga rana irin ta yau.
Peter Obi ya yi wa mutane karin bayani
Sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwar da tsohon ‘dan takaran shugaban kasar ya aikawa Gowon ya jefa shi a cikin matsala.
A karshe sai da ‘dan siyasar ya fito ya sake jawabi, ya na bayyana abin da ya sa aka ji ya na taya Gowon murnar cika shekara 90 a shafin X.
Masu yabon Tinubu sun koma kuka
Ku na da labarin cewa Joe Igbokwe da aka sani wajen yin raga-raga da makiyan Bola Tinubu ya na cikin masu kuka da APC a yau.
Sukar gwamnatin Bola Tinubu ne ya jawo Sanata Ali Ndume ya rasa matsayinsa a majalisa duk da yana cikin manyan a APC.
Asali: Legit.ng