"Babu Wanda Ya Isa:" Abba Ya Yi Martani kan Hana zaben Ƙananan Hukumomin Kano

"Babu Wanda Ya Isa:" Abba Ya Yi Martani kan Hana zaben Ƙananan Hukumomin Kano

  • Gwamnatin Kano ta ce ba za ta bar wasu tsirarun mutane su kawo cikas ga zaben kananan hukumomi a ranar Asabar ba
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce za a yi zabe a Kano duk da kotu ta haramta gudanar da zaben bisa wasu dalilai da ta zayyana
  • A ranar Asabar 26 Oktoba ne hukumar zabe mai zaman kanta ta KANSIEC ta ce za a yi zaben kananan hukumomi 44 na jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta yi martani kan hukuncin babbar kotun tarayya na haramta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar.

Kara karanta wannan

'Za mu mutunta doka,' ƴan sandan Kano sun dauki matsaya kan shiga zaben ciyamomi

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fadi matsayar gwamnatinsa kan hukuncin lokacin da ya mika tutar NNPP ga 'yan takara a kananan hukumomi 44.

Jihar Kano
Gwamnatin Kano ta jaddada za a gudanar da zaben Ciyamomi ranar Asabar Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ce za a gudanar da zabe babu gudu babu ja da baya duk da akwai masu neman hana zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya zargi yan adawa da neman hana zabe

PM News ta tattaro gwamna Abba Kabir Yusuf ya zargi wasu yan adawa da kokarin kawo cikas wajen gudanar da zaben kananan hukumomi a Kano.

Gwamnan ya bayyana haka ga dandazon magoya bayan NNPP a filin wasa na Sani Abacha yayin kaddamar da yan takarar jam'iyyar.

Gwamna Abba ya fadi matsayarsu kan zabe

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano na da goyon bayan doka wajen gudanar da zaben kananan hukumomi a gobe Asabar

Kara karanta wannan

Kano: Duk da kotu ta taka birki, Hukumar KANSIEC na shirin zaben Ranar Asabar

Ya jaddada cewa gwamnati za ta ba hukumar zaben dukkanin goyon baya, sannan ba za a lamunci duk wani abu da zai lalata zaman lafiya da jihar ke mora ba.

Yan sanda sun ki shiga zaben Kano

A baya mun ruwaito cewa rundunar yan sandan Kano ta ce za ta bi umarnin kotu wajen kin shiga zaben kananan hukumomi da hukumar KANSIEC za ta gudanar a ranar 26 Oktoba, 2024.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana matsayarsu, amma ya ce jami'ai za su fito domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.