Dalilin Bola Tinubu Na Korar Ministoci 5 Ya Bayyana, An Faɗi Asalin Abin da Ya Faru
- Fadar shugaban ƙasa ta ce ba haka kurum Tinubu ya zabi wasu ministoci ya kora ba, sai da aka tantance aikin kowane ɗaya daga ciki
- Hadimin shugaban, Bayo Onanuga ya ce Hadiza Bala Usman ce ta jagoranci tantancewa bisa la'akari da ra'ayoyin ƴan Najeriya
- Bola Tinubu dai ya kori ministoci biyar ranar Laraba, sannan ya haɗa da dakatacciyar ministar jin kai watau Dr. Betta Edu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya yi wa majalisar zartaswa garambawul, inda ya sauke ministoci biyar bisa la’akari da yadda al’umma ke kallon ayyukansu.
Mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya ce ba haka kurum Tinubu ya kori ministocin ba.
Onanuga ya ce Tinubu ya yi garambawul ne bayan dogon nazari kan rahoton tantancewar da Hadiza Bala Usman, mai ba shi shawara kan tsare-tsare ta jagoranta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin shugaban ƙasa ya yi wannan furucin ne a wata hira da gidan talabijin na Arise tv ranar Alhamis.
Yadda Tinubu ya faɗawa ministoci shirinsa
Bayo Onanuga ya ce wannan ya nuna shugaba Tinubu bai zo da wasa ba domin wannan na cikin shirinsa tun bayan naɗa ministocin a bara.
Ya tunawa jama'a cewa a watan Agustan 2023 a wurin bikin rantsar da su, Tinubu ya bayyana cewa yana da karfin ikon naɗawa da korar ministoci.
Ƴa kuma gargaɗe su cewa ba zai yi wata-wata ba ko jin ƙyashin korar duk ministan da ya gaza yin ayyukan da suka rataya a wuyansa, Vanguard ta kawo labarin.
Matakan da Tinubu ya bi wajen korar ministoci 5
Idan za ku iya tunawa Tinubu ya ba Hadiza Bala Usman aikin kula da aikin tantancewa, wanda ya hada da tattara ra’ayoyin jama’a kan ayyukan ministocin.
"Hadiza ta bullo da wani tsarin fasaha na zamani, inda ta nemi ƴan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan ƙoƙarin ministocin."
"A karshe dai sakamakon ya dogara ne da hujjoji masu ma'ana da kuma ra'ayoyin ƴan Najeriya kan nagartar ministocin, ba ruwan Tinubu shi kawai ya aiwatar da abin da jama'a suka yanke."
- Bayo Onanuga.
Jerin ministocin da aka kora da jihohinsu
A wani labarin kuma kun ji cewa ministoci biyar suka rasa muƙamansu da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi garambawul a majalisar zartaswa ranar Laraba.
Legit Hausa ta tattaro muku cikakken jerin sunayen ministocin da shugaban ƙasa ya kora, ma'aikatu da kuma jihohin da suka fito.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng