Jam'iyyu Sun Haɗu Sun Ragargaji Tinubu kan Korar Ministoci

Jam'iyyu Sun Haɗu Sun Ragargaji Tinubu kan Korar Ministoci

  • A ranar Laraba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kori wasu daga cikin ministocinsa a wani shiri na gyara tafiyarsa
  • Wasu yan siyasa suna ganin korar ministocin ba zai tsinana komai ba wajen gyara tafiyar shugaban kasar musamman kan tattali
  • Mataimakin shugaban matasan PDP na kasa, Timothy Osadolor ya bayyana cewa korar ministocin kora kunya da hauka ne kawai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Korar ministoci da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ya fara jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin yan siyasa.

Jam'iyyun adawa sun soki shugaban kasar kan cewa ya kamata ya kara korar da yawa daga cikin ministocinsa idan da gaske yake.

Kara karanta wannan

Ministoci sun firgita da dawowar Tinubu, an fadi lokacin da ake ganin zai kori wasu

Tinubu
Yan adawa sun soki Tinubu kan korar ministoci. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa rahoto kan yadda manyan yan adawa a Najeriya suka yi maratani kan korar ministoci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta ce Tinubu ya yi kora kunya

Mataimakin shugaban matasan PDP na kasa, Timothy Osadolor ya ce yan Najeriya ba canza ministoci ko ma'aikatu suke bukata ba.

Osadolor ya ce yan Najeriya na bukatar tsaro, ayyukan yi da cigaba amma shugaban kasa ya kori ministoci saboda kora kunya kan gazawa da ya yi.

'Ba ka dauko hanya ba' - SDP ga Tinubu

Shugaban SDP na kasa, Shehu Gabam ya ce sauya sunan ma'aikatu da korar wasu ministoci ba hanyar gyara ba ce.

Shehu Gabam ya ce kusan dukkan waɗanda suke kewaye da Tinubu ba za su iya taimaka masa wajen ceto Najeriya ba.

Saboda haka ya ce idan gyara ake so ya zama wajibi Bola Tinubu ya kori kaso 75% na ministocinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga ofis bayan hutu, talakawa sun tura masa bukatu

LP ta ce a kori yunwa ba ministoci ba

Sakataren yada labaran LP, Obiora Ifoh ya bayyana cewa ba sauya sunan ma'aikatu da ba su da alaka da tattali ne babban abin da yan Najeriya ke bukata ba.

Ifoh ya ce ya kamata shugaban kasa ya fito da tsare-tsaren tattali da za su rage yunwa a Najeriya da samar da ayyuka.

Tinubu ya tura sako ga korarrun ministoci

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya tura sako na musamman ga ministoci biyar da ya sallama daga aiki.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ministocin da ya kora fatan alheri a rayuwar da za su yi a gaba tare da yi musu godiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng