Jerin Ministocin da Tinubu Ya Kora daga Aiki da Jihohin da Suka Fito a Najeriya
- Ministoci 5 ne suka rasa muƙamansu da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi garambawul a majalisar zartaswa ranar Laraba
- Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin korar ministocin ne bayan taron majalisar zartaswa FEC a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
- Hakan dai wani ɓangare ne a yunƙurin shugaban kasar na yi wa ma'aikatu kwaskwarima a gwamnatinsa bayan kusan shekara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - A jiya Laraba ne shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sallami ministoci biyar daga aiki.
Kafin haka Shugaba Tinubu ya sanar da rusa ma'aikatar raya yankin Neja Delta da ma'aikatar kula da harkokin wasanni duk a ƙoƙarin yin garambawul.
Hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a shafin X, inda ya ce Tinubu ya kirkiro ma'aikatar ci gaban yankuna da za ta kula da harkokin Neja Delta da sauran yankuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya kuma sauke ministoci biyar bayan taron majalisar zartaswa ta ƙasa watau FEC a Abuja ranar Laraba, 23 ga watan Oktoba, 2024.
Ministar harkokin mata, Barista Uju-Ken Ohanenye, da Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman su ne manya daga cikin waɗanda aka kora daga aiki.
Ministocin da Tinubu ya sauke da jihohinsu
1. Ministar harkokin mata, Barista Uju-Ken Ohanenye (jihar Anambra).
2. Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman (jihar Adamawa).
3. Ministar harkokin yawon buɗe ido, Lola Ade-John (jihar Ekiti)
4. Ƙaramin Ministan gidaje ɗa raya birane, Abdullahi Muhammad Gwarzo (jihar Kano).
5. Ministar harkokin ci gaban matasa, Jamila Bio Ibrahim (jihar Kwara).
A karshe, Shugaɓa Tinubu ya masu fatan alheri da godiya bisa aikin da suka yi wa ƙasa a tsawon lokacin da suka ɗauka kan muƙamansu.
Bola Tinubu ya maye gurbin Betta Edu
A wani rahoton kuma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin Betta Edu, dakatacciyar ministar harkokin jin ƙai da yaye talauci.
Shugaban ƙasar ya naɗa Dr Nentawe Yilwatda a matsayin sabon ministan jin ƙai, wanda zai maye gurbin Betta Edo bayan dogon lokaci da dakatar da ita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng