Rikicin PDP: Daga Karshe An Fadi Yankin da Zai Samar da Shugaban Jam'iyyar Na Kasa
- Ana ci gaba da shirye-shiryen wanda zai karɓi ragamar shugabancin jam'iyyar PDP na ƙasa daga hannun Umar Iliya Damagum
- Tsohon sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa ya bayyana cewa yankin Arewa ta Tsakiya ne zai samar da wanda zai canji Damagum
- Ya bayyana cewa an cimma wannan matsayar ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da aka gudanar a ranar Talata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, Kola Ologbondiyan, ya bayyana yankin da shugaban jam'iyyar wanda zai maye gurbin Umar Damagum zai fito.
Kola Ologbondiyan ya ce ce shugabannin jam’iyyar sun yanke shawarar cewa yankin Arewa ta Tsakiya zai fitar da ɗan takarar da zai karɓi mukamin shugaban jam’iyyar na ƙasa a lokacin taron NEC na watan Nuwamba.
Tsohon sakataren yaɗa labaran na PDP ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na safiya a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga ina shugaban jam'iyyar PDP zai fito?
Ologbondiyan ya ce shugabannin PDP sun cimma matsayar hakan ne a taron da suka yi na ranar Talata, suka sanar da ɗage taron majalisar zartaswa na ƙasa (NEC) zuwa watan Nuwamba.
Ya ce sun amince cewa Arewa ta Tsakiya zai samar da wanda zai maye gurbin tsohon shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu wanda ya fito daga yankin.
"Dalilin ɗage taron shi ne don ba shugabannin jam’iyyar damar lashe zaɓe a jihar Ondo."
"A bisa hakan mambobi sun kwantar da hankulansu saboda yanzu ta tabbata cewa bayan nasara a Ondo, a ranar 28 ga Nuwamba za a yi taron NEC inda yankin Arewa ta Tsakiya zai samu damar samar da wanda zai maye gurbin Ayu."
"Daga cikin abin da aka tattauna kuma aka cimma matsaya a daren jiya shi ne a ranar 28 ga watan Nuwamba, yankin Arewa ta Tsakiya zai samar da wanda zai maye gurbin Ambassada Umar Iliya Damagum. Zan iya faɗin hakan a ko'ina"
- Kola Ologbondiyan
Gwamna ya amince da shugabancin Damagum a PDP
A wani labarin kuma, kun ji gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi amai ya lashe, ya amince da shugabancin Umar Damagum a jam'iyyar PDP.
Shugaban na ƙungiyar gwamnonin PDP ya yi mubayi'a ga shugabancin Damagum ne a wani taron masu ruwa da tsakin jam'iyyar a birnin tarayya Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng